YUHANASU ABDULMUMIN Ita ce wacce ta haifi wani jariri amma kuma lamarin ya zo da ban mamaki da al’ajabi, domin kuwa ta haifi jaririn ne dauk...
YUHANASU ABDULMUMIN Ita ce wacce ta haifi wani jariri amma kuma lamarin ya zo da ban
mamaki da al’ajabi, domin kuwa ta haifi jaririn ne
dauke da Alkur’ani da carbi a makale bisa wuyan
yaron. Wannan lamarin ya jefa jama’ar garin na
Burga cikin shakku inda wasu ke cewa karya ce
a yayin da wasu kuma suka nuna gamsuwarsu kan lamarin. A bisa haka ne aka kawo matar da
jaririnta wajen Shaikh Dahiru Bauci a ranar
Juma’ar nan domin jin me zai ce kan wannan
lamari. A bisa haka ne wakilinmu KHALID IDRIS DOYA ya samu ganawa da ita kan wannan abun mamakin ga kuma abun da take cewa kan
wannan haihuwar tata daki-daki. Ki gabatar mana da kanki? Sunana Yuhanasu Abdulmumin daga Burga, a
karamar hukumar Tafawa Balewa, shekaruna 30
da haihuwa, ina da miji da ‘ya’ya bakwai. Ga ki da wannan al’amari na abun al’ajabi na haihu da kika yi na yaro dauke da Kur’ani da kuma carbi ya hakan ta faru? A ranar Laraba ne na haifi wannan jaririn nawa,
kuma tare da wannan Kur’ani da kuma carbin. Kina nufin ke nan carbi da Kur’anin ya fito daga cikin-cikinki ke nan? Eh, da hakan na haife shi tare da shi, daga cikin-
cikina tare da Kur’ani da carbin na haifi yaron
nawa. A gida kika haihu ko kuma a asibiti? A gida na haihu, daman a washe garin ranar
Laraba mun tsara cewar za mu zo cikin Bauci
asibiti domin cikin ya wuce wata taran da ya
kamata na haihu; daman mun tsara cewar za a
kawo ni asibiti domin a yi min tiyata tunda lokacin
da ya dace na haihun ya wuce kuma ga shi ina ta laulayi cikin na wahalar da ni. Wannan dalilin ne
ya sa muka so a zo asibiti, sai a ranar Talata daren
ranar Laraba (da Asubahi) sai Allah ya nufa kuma
na haihu da kaina tare da wannan Kur’ani da
carbin a wuyansa, shi Alkur’ani din yana manne a
jikin jaririn barin wuyansa. Wace ce ta amshi haihuwar (Ingozoma)? Ni dayana na haihu, babu wacce ta karbi
haihuwar, bayan da na haihu ne sai wadannan
yaran (‘ya’yanta) suka ji kukan jaririn sai suka
kira makwafciyarmu a cikin gida, suka fada mata
cewa mamarmu ta haihuwa, tana isowa sai ta
duba domin daya yaron sai take cewa ai kun yar masa ma da jaka a kansa. Nan take ta kai hanu
domin dagawa a zatonta jaka ce sai ta ga abun ya
tashi manne da wuyan yaro har da carbi da
Kur’anin a manne a jikinsa, nan take ta yi salati ta
fita domin shaida wa jama’ar gari. Mai gidana ya je
masallaci aka tarar da shi aka yi masa bayanin abun da ke faru, sai ya zo ya gani, ya ce, bari ya je
masallaci ya sanar. Da aka zo aka duba sai aka
samu Kur’ani ne da casbaha a wuyan yaron ya
nade jaririn. Mai gida ya ce, a sanar da limami
jama’a su zo, sai limamin da aka kira bai zo ba; da
bai zo ba sai Sarkin Malamai ya zo ya ga yaron da abun da na haifa tare da jaririna, nan take ya ga
Kur’ani ne da ya duba. Shi kuma liman da ya zo
sai ya ce a ciro masa Kur’anin a kai masa ya gani,
da aka cire aka kai masa ya duba sosai sai ya ce
eh tabbas Kur’ani ne. Amma kuma sai liman din
ya ce, ya za a yi a ce an haifi yaro da Kur’ani a cikin najasa? Kur’ani bai fita a cikin najasa,å da ya
fadi hakan na cewa Kur’ani ba ya fita a cikin
najasa sai wani da AsΩuba ya dauki lasifika sai
yana wa’azi yana cewa Allah ya tsine mana, Allah
yai mana… Yana ta fada dai, wai a cewarsa idan
har Kur’ani zai fita a cikin cikina tare da jariri Allah ya tarwatsa shi. Nan take sai kai ya rabu biyu,
wasu suna karyata lamarin wasu kuma suna
cewa sun gamsu da abun. Masu cewa ba su
gamsu ba har suka iya rinjayar mai gidana, suka
yi ta cewa wai aljanu ne suka rataya masa
wannan jakar (Kur’ani). Da kika haihun ya kika ji? Gaskiya ni a lokacin da na haihu na fita daga cikin
daga cikin hayyacina, masu daukan hotu suna ta
dauka da daukar hotunansu a lokacin da na
haihun, domin a lokacin da na haihun ana
sanarwar kawai sai jama’a suka yi ta shigowa
cikin gidana suna ta daukar hotuna, a lokacin da suke wannan dauke-dauken hotunan ma ko
wanka ba a yi masa (jaririn) ba; domin shi
wannan yaron nawa na haife sa a jikinsa babu
jini babu ruwa. Babu jinin haihuwa babu ruwa kuma? Eh, babu jini ko ruwa haka na haife sa, cibi ne
kawai da aka yanke masa aka ga jini, amma
yadda na haife sa babu jini a cikinsa. A lokacin da kike kokarin haihuwar wannan jaririn kin ga wani canjin yanayi da sauran haihuwarki ta baya ne? Gaskiya kam, na ji canjin yanayoyi da daman
gaske sabanin wadanda nake ji a haihuwar da na
yi a baya, na farko da wannan yaron ya wuce
wata tara, na biyu kuma na kan ji numfashin
jaririn har cikina yana rawa. Har ma nake cewa
matan cikin gidanmu ni kam a wannan karon ko na haihu ko kuma na mutu a bayyana ma
wannan yaron dan cikin nawa da cewa shi dan
baiwa ne. domin tun da fari ma wannan yaron
mahaifinsa ya bukaci na zubar da cikin yaron
nan, a cewarsa shi ya gaji da jinya wai bai da
kudin jinyar wannan laulayin jaririn, ya ce, min idan ban zub da cikin ba yanzu na fara jin zafin
laulayi, idan kuma na je asibiti a dauki hotun
(scanning) sai kuma na daina jin motsin yaro,
amma kuma cikin nawa na kara girma sosai; sau
biyu ina zuwa awo a cikin Bauci ana shaida min
cewar yaron na da rai kuma yana motsi, amma ni ne ba zan ji ba, na ce musu ni gaskiya ban taba jin
haka ba a sauran haihuwar da na yi ta yi a baya,
kuma ga shi na wuce wata tara har na shiga na
goma ban haihu ba; kuma ma bayan nan
wannan yaron na haife sa ga shi ya fito kato,
hankali ya fara tashi, cikin ikon Allah kuma sai ga abun da na haifa. Mijinki ya bayyana cewa ki zubar da cikin don bai da kudin jinya, yanzu da kika haifi jariri da Kur’ani ya yi farin ciki ko yaya? Ya yi farin ciki da wannan haihuwar sosai, amma
da ‘yan karyatawa suka ce babu yadda za a yi a
haifi yaro da Kur’ani suka yi tasiri a zuciyarsa, sai
ya zama ‘yan Izala suna ta zaginsa a gari, ni ma
haka, sai kuma su ‘yan Darika suka yi ta zuwa
suna daukar hotunsa suna cewa ranar suna za su yi masa zikiri sun yarda da abun da Allah ya aiko
da shi. Sun soma zuwa a ranar suna da nufin za
su yi zikirinsu sai mahaifin yaron ya ce musu su
tafi kawai an dauke ranar suna, su kuma suka
nace sai da suka yi wannan zikirin suna murna
(‘yan Darikan ke nan), ’yan Izala kuma na kushewa. Wane suna kika sanya masa kuma wannan
haihuwar taki ta nawa ce? Na sanya masa suna Muhammad Auwal, wannan
haihuwar tawa ta bakwai ke nan, dukkaninsu
kuma suna raye, sai dai haihuwata ta farko
tagwaye (‘yan biyu) na haifa, mace da na miji sai
na mijin ya rasu ya bar macen tana nan tana raye. Daga karshe to me za ki ce kan wannan haihuwar taki? Ni dai gaskiya ga abun da na haifa kuma ba na ja
da ikon Allah, Allah zai iya komai a kaina,
wannan kuma abun aljabi ne da ya wakana a
kaina.
.
Source ©Leadershipayau
COMMENTS