Wani dan yawo bude ido dan kasar Faransa ya buga kirjin cewa, ya yi wa mata fiye da 600 ‘yan Afrika ciki a cikin shekara 2, Jean Micheal dan...
Wani dan yawo bude ido dan kasar Faransa ya
buga kirjin cewa, ya yi wa mata fiye da 600 ‘yan
Afrika ciki a cikin shekara 2, Jean Micheal dan
shekara 40 ya yi wannan fallasar ne ta wata kafar
sadarwa ta intanet mai suna “Africa24”. Kasashen
da ya kewaya domin yin wannan ta’asar sun dada da Nijeriya da Kamaru da Ibory Coast da
Togo da Ghana da kuma kasar Guinea. Yawancin ‘yan Afrika na ganin fararen fata a
matsayin mutane ne masu dukiya wadanda za su
iya canza rayuwarsu, saboda haka, a kan samu
saukin yaudaransu a yi amfani dasu yadda a ke
so. Simon Ateba daga Washington District of
Columbia a ne ya fassara bayanin daga harshen
faransanci. “Barkan ku da safiya “Africa 24”, Ina da bayanin
da nake son yi a kan barnar da na tafka a
kasashen Afrika 6 cikinsu a kwai Kamaru da
Togo da Cote D’Iboire da Nijeriya da Ghana da
kuma kasar Guinea. Ba wai ina alfahari da abin da
na yi ba ne amma wani abu ne daya faru kuma abin takaici ne. “A kasar Faransa inda na taso ni talaka ne kwarai
bani da kudi ko kadan, sai wata rana na buga
caca in da na ci Euros 550, wadanna sune kudi
mafi yawa dana taba rikewa a rayuwa ta” “Na rasa abin da zan yi da kudaden sai wani
aboki na ya bani shawarar tafiya kasashen
Afrika, bayan na hada dukkan takardun da suka
kamata, kasar farko da muka ita ce kasar Ibory
Coast. “A Abidjan babban birnin kasar Ibory Coast, a
nan ne muka kama hayar daki tunda muna cikin
kudi, muka yi abota da ‘yan kasar, su suka hada
mu da ‘yanmatan kasar daga nan ne fa al’amarin
ya fara gadan-gadan” “A nan ne na fara jima’i da ‘yan matan Afrika, a
kullum na kan kwanta da ‘yan mata uku a lokaci
daya, na ji dadin lamarin kwarai” “Ban damu da lafiyata ba ko kadan, ni da aboki
na kullum mu kan fita yawo cikin gari domin
tsamo mata da zamu kwanta dasu” “A kwai lokacin da na hadu da wata yarinya, nan
take ta nemi in aureta wai a shiye take ta dauki
ciki da ni, ban san ko kudi ke yaudaransu ko
kuma kasancewa na bature ke jawo hankalinsu
gare ni ba” “Na kashe fiye da Euros 60 a kasar Ibory Coast, in
da cikin wata uku na kwanta da mata fiye da 80. “Daga kasar Ibory Coast sai na wuce kasar Togo
in da na kwanta da mata fiye da 100 tare da
kashe Euros 40,000, wata uku kwai na yi a Togo
sai na wuce Nijeriya” “A Nijeriya ne na fi samun ‘yan mata, duk da ban
iya turancin Ingilishi ba amma ‘yan matan Nijeriya
na matukar son Turawa” “A Nijeriya na kama hayan cikakken gida a garin
Legas na tsawon wata shida na kashe akalla
Euros 100,000 na kuma yi jima’i da ‘yanmata har
230. Lallai na ji dadin Nijeriya, saboda akwai mata
sosai kuma suna da saukin harka.” “Daga Nijeriya sai na wuce kasar Ghana daga nan
na zarce kasar Kamaru na karkare a kasar. “Na share fiye da shekara daya a wadannan
kasashe na kuma kashe fiye da Euro 200,000,
ina kuma mai tabbatar maka da cewa, na yi jima’i
da ‘yan mata fiye da 700 a tsakanin wannan
lokacin. “Gaba daya na yi jima’i da mata fiye da 1,400 a
kasashen Afrika 6 da na zagaya, ina tattare da
hotunan su dukka da ranan da muka hadu da
kuma lambar wayar su. Shafi na musamman na
bude a “Facebook” saboda su” “Tun da na dawo gida Faransa na samu labarin
kusan ‘yan mata 600 daga cikin wadanda na yi
mu’amala dasu su dauki ciki, wasu sun zubar da
cikin ban kuma san yawan wadanda suka haihu
ba a cikin su. “Nahiyar Afrika na da dadi, a kwai kyawawan
mata wanda a shirye suke kuyi mu’a,mala na jin
dadi matukar kana da kudi ko kuma kai farar fata
ne” “Na kuma lura ‘yan matan Afrika na matukar son
haihuwar yaran da sukan kira “Half Cast” ban san
dalilin hakan ba amma kuma da yawan su za su
iya yin komai don ka yi musu ciki, Euros 100 kudi
mai yawa a Afrika” “A takaice, na yi zagayen shakatawa na shekara
2 a yankin Afrika in da na kwanta da mata 1,400,
600 daga cikin su sun yi ciki”. “Na san mutane da yawa za su yi ta zagi na amma
zagin ku ba zai bata mani rai ba, na san dai lallai
na ji dadin zaman da na yi a Afrika, ina kuma
shirin wani balaguron kwanan nan, ina sa ran
shiga kasashen Senegal da Mali da Gabon da
Benin da Niger da kuma kasar Kongo” “Ranar da na dawo Faransa, kai tsaye na wuce
asibiti na yi gwajegwaje inda aka tabbtar mani da
cewa, bana dauke da cutar HIB ko kuma wasu
kananan cututtukan da ake dauka a wurin jima’i,
shi ma abokin tafiya ta lafiyar sa lau, muna kuma
sake shirya wani tafiyar kwanan nan, kar ka damu da kurakuran da zaka gani a cikin
rubutuna hakan ya faru ne saboda ko karatun sakandare ban kamala ba.
©hausaleadership
COMMENTS