Tsohon gwamnan Jihar Jigawa, kuma daya daga cikin masu neman Jam’iyyar PDP ta tsayar da su neman Shugabancin Kasarnan, Sule Lamido, ya ce, b...
Tsohon gwamnan Jihar Jigawa, kuma daya daga
cikin masu neman Jam’iyyar PDP ta tsayar da su
neman Shugabancin Kasarnan, Sule Lamido, ya
ce, ba wanda ya isa ya hana shi zama Shugaban
kasarnan a zabe mai zuwa. Lamido, ya yi wannan furucin ne a wajen wani
taro na bude Ofishin kamfen din shi na neman
Shugabancin kasa a Birnin Kudu, ta Jihar Jigawa.
Idan har nufin Allah ne, ba wanda zai iya hana ni
kasancewa Shugaban kasan nan. Ya kuma bayyana cewa, shakka ba bu, za a fafata
neman Shugabancin kasar nan ne a shekarar
2019, a tsakanin wadansu mutane biyu, duk
cikansu Musulmai, Fulani, tsaffin gwamnoni
sannan kuma tsaffin Ministoci a kasar nan a
lokuta daban-daban. “Kai ba bu fa wani dan adam a doron duniyar
nan, wanda ya isa ya hana nufin Allah, idan har
Allah Ya nufa ni ne zan kasance Shugaban
wannan kasar, ko ta hanyar Kotu, ko ta wace
hanya, ba wanda ya isa ya hana ni. “Bambancin da ke Tsakani na da Buhari shi ne,
duk da ya taba zama gwamna a karkashin
mulkin Soja, amma dai bai yi wa mutane aiki ba.
Ya kuma yi Ministan Man Fetur, wanda mutane da
yawa ma ba su san hakan ba. Alhalin ni, a lokacin
da na yi Ministan harkokin waje, duk duniyan nan kowa ya sanni, sannan kuma, ayyukan da na
yi a shekaru takwas na zama na a kujerar
gwamna, sun isa shaida a gare ni. Sule Lamido, ya kara da cewa, Shugaba
Muhammadu Buhari, Bafillatani ne kadai da
sunan an haife shi Bafillatani, daganan, sai ya
kalubalanci Shugaba Buhari da ya fassara masa
wasu ‘yan kalamai da ya yi zuwa Fullanci a wajen
taron. “Buhari da Jam’iyyar sa ta APC, ba karyar da ba su
shararawa al’ummar Nijeriya ba a lokacin zaben
2015, to yanzun mutane sun san gaskiyar
lamurra, za kuma su ba su amsa a zaben 2019,” duk in ji Sule Lamido.
©hausaleadership
COMMENTS