Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya sanar cewa daga yanzu zai ladaftar da jami’an tsaron kasar idan har aka sake sace wasu dalibai a kasar...
Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya sanar
cewa daga yanzu zai ladaftar da jami’an tsaron kasar idan har aka sake sace wasu dalibai a kasar.
‘Na umarci duk jami’an tsaro da su tabbatar da an samu cikakken tsaro a makarantun kasar’ inji
Shugaba Buhari.
Shugaba Buhari ya kara da cewa, duk masu siyasantar da harkar tsaron Kasar nan sai gwamnati ta hukunta su.
Shugaba Buhari ya bayyana hakanne a jiya juma'a yayin da yake ganawa da dalibai da
iyayen ‘yan matan sakandaren Dapchi da aka sako.
.
©Leadershipayau
COMMENTS