BILKISU MUHAMMAD, yarinya ce ‘yar shekaru 20, a wannan tattaunawa da ta yi da LEADERSHIP A YAU, ta bayyana yadda aka yi auren auren dole ya ...
BILKISU MUHAMMAD, yarinya ce ‘yar shekaru 20, a wannan tattaunawa da ta yi da LEADERSHIP A YAU, ta bayyana yadda aka yi auren auren dole ya janyo mata fada wa gidan kurkuku. Wakilinmu Umar Faruk ne ya yi tattaunawar kamar haka: Mene ne tarihinki a takaice? Alhamdullahi, suna na Bilkisu Adamu ni dai
mutuniyar karamar hukumar Argungu ce a jihar
Kebbi. Shekarunki nawa? Shekaruna 20 da haihuwa a duniya. Malama Bilkisu ya maganar makaranta? Na yi karatun Islamiyya har na sauke Alkur’ani
tun ina ‘yar shekara goma sha hudu da haihuwa
a makarantar Mallam Boye cikin garin Argungu.
Sannan na yi makarantar Firamare, amma ban
kammala ba na cewa iyayena ba na so
makarantar Firamare, na fi son makarantar islam`iyya wadda ita ce na yi har na sauka
Alkur’ani. Mene ne ya hana ki shiga makarantar boko? Ka san duk abin da ba ka da ra’ayi akan sa ba za
ka yi shi ba, amma da a ce ina da ra’ayin yin boko
da na yi shi. Domin ka ga karatun Islamiya da
nake da ra’ayi da sha’awa na tsaya na yi. Mene ne ya kawo ki wannan gidan kurkuku?
Sanadiyar auren dole, saboda wani ne mai suna
Shehu yan so na sosai, na nuna masa ba na son
sa kuma na gaya masa ka da ya kara zuwa
gurina da sunan yana sona, amma iyayena sun
nuna min lallai ala tilas sai na aure shi, duk kuwa
da irin dagewa da na yi cewa ban a son shi. Tun da Shehu ya ji cewa na gaya masa cewa bana
son sa, sai ya ce mani duk ranar da ya kara zuwa
gurina sai na ce ina son shi, wanda hakan ta faru
domin ranar da ya dowa gidanmu, ranar wata
Jama’a da misalin karfe 3 na rana, ko da ya zo
gidan namu ya same ni kaina a sunkuye sai ya ce, domin Allah koda ba na son shi, na tada kaina na
kalle shi, ko da na tada kai na kalle shi sai kawai
na ji cewa ba zan iya korar sshi ko na yi masa
wulakanci ba, kai har ma na ji cewa ko wani ya ce
zai takura masa ba zan yarda ba. Menene yasa kike gudun gidan mijin naki bayan an yi aure? Tau! tun farko na gayawa iyayena da kuma shi
Shehu cewa ba na son shi, saboda an tilasta mani
yin auren dole. Na yi tunanin cewa iyayena za su
yi la’akari da kuma nazari kan maganar da na
fada musu cewa ba na son shi, amma kuma ba su
iya daukar matakin da ya dace ba. Sai daga baya na fada wa iyayena cewa ga fa abin da Shehu ya
gayama ni lokacin zuwansa na farko a gidanmu
inda ya ce, duk ranar da ya dawo gidanmu sai na
ce ina son shi. Saboda wannan magana da Shehu
ya yi sai na fara tunanin cewa wani abu zai faru
da ni ko da iyayena. Ka ga ko abin da zuciya ta ke nuna mani ya faru, domin iyayena sun yi mani
aure da shi kuma ga abin da ya biyo baya
sakamakon rashin kyakyawa naziri. Inda na kasa
zaman gidan aure, wanda koda yaushe, idan zai
fita zuwa wurin aikinsa, sai na gudu zuwa gidajen
kawayena. Wane wuri ne kike zuwa idan kin gudu? Akwai wata kawata mai suna Hindatu, gidansu
nake guduwa, wadda ake tuhumar cewa ita ce
ke boye ni. Bayan na je gidan nasu ban same
taba sai na wuce zuwa wurin wani abokin
saurayinta mai suna Zayyanu, sai na ce masa don
ko ya ga Hindatu. Zayyanu ya ce bai gan ta, kuma ya tabbatar ba su tare da saurayinta natam watau
abokinsa ke nan. Daga nan Zayyanu ya sa kayansa zuwa Masallaci
domin Juma’a ce, can sai ga jami’an NSCDC na
neman shi Zayyanu kan ya karbi belin wani
abokinsa da ake ce wa Obi. Sai jami’an suka kama
ni da cewa Zayyanu ke boye ni. Daga nan suka
bani tsoron cewa in ce shi ke boye ni, kuma a cikin dakinsa aka kama ni a tsaye daga ni sai
bireziya da dogon wando, ko a bani kashi kuma
su kai ni gidan kurkuku. Sai na ce ni ba zan taba
yi wa wani sharri ko kazafi ba. Daga nan sai suka
dauke ni zuwa ofishinsu da ke garin Argungu,
bayan na kwana daya a ofishinsu sai suka cika takardar kara zuwa kotu, wadda ban san me
suka rubuta ba tun da ban yi makarantar boko
ba. Shekarun ki nawa da yin Aure? Aurena bai shekara ba, domin bai wuce wata
hudu zuwa biyar ba wannan matsalar ta faru. Menene tsawon zaman ki a gidan kurkukun Argungu? Na zauna gidan kurkukun na garin Argungu
tsawon sati uku, kafin babbar mai shari’a kuma
cif jojin jihar ta Kebbi, Maishari’a Elizabeth Asabe
Karatu ta ziyarar ci gidan kurkukun Argungu a
ranar Laraba 16 ga wata Nuwamba, 2017, inda ta
gana da dukkan mazauna a gidan kurkukun ta kuma bada umurnin cewa a gabatar da takardun
dukkan wadanda ke a cikin gidan daya bayan
daya. Ni kadai ce mace a gidan, bayan an karanta
matsalar da yasa aka kawo ni sai ta yi mani afuwa
kamar yadda ta yi wa wasu. Ka ga da ba don
wannan ziyarar ba, da ban san makomata ba. Kuma kaga koda nake zaman kurkuku bani da
aure da shi mijin dole da iyayena suka yi mani. Wane irin kalubale kika fuskanta a zaman ki a gidan kurkuku? Ban gamu da gallazawa ko takura a gidan
kurkukun ba, amma dai kalubalen shi ne auren
dole aka yi mani, kuma shi ne ya zama sanadiyar
na zauna gidan kurkukun; bugu da kari ya bani
saki uku saboda sakin mace yana da zafi wanda
shi ne kawai zan iya tuna wa na ji bakin ciki da bacin rai a rayuwata. Wani irin darasi ki koya yayi zamanki kurkukun? Darasin da na koya shi ne cewa, gidan kurkuku
ba wurin da ya kamata a ce mutanen kirki da
mutunci da kuma imani ya shiga ba, saboda wasu
dalilai da ba na son in bayyana su. Ba na fatan
wani ko wata su shiga gidan kurkuku, ko ni na
dauki wannan a matsayin wata kaddara da Allah ya rubuto da ni cewa za ta faru da ni. Menene kiranki ko shawara ga iyaye? Na ji dadin wannan tambaya da ka yi min, saboda
mafi akasarin abin da ke sa ‘yan mata na shiga
wani hali yana faruwa ne da sanadiyar iyaye suna
suna yi wa ‘ya’yansu auren dole, wanda sun san
cewa yaransu ba sa son ma mijin amma sai ka ga
an yi tsaye sai ‘ya ta auri mijin da ba ta so, wanda shari’ar Musulumci ma ba ta yarda da auren dole
ba. Saboda hakan don Allah iyayenmu ku dawo
da tunininku. Babu wada za ta son in ‘yarta ta
fada irin halin da na shiga. Har ila yau, wasu
iyayen kwadayin kudi ne ke san su yi wa ‘ya’ya
auren dole, saboda haka ina kira gare su da su daina wannan dabi’a.
©hausaleadership
COMMENTS