Wata ‘yar kunar bakin wake wadda ake kyautata mata zaton ‘yar kungiyar Boko Haram ce ta auka wa masu ibada a cikin massallaci a Falatari da ...
Wata ‘yar kunar bakin wake wadda ake kyautata
mata zaton ‘yar kungiyar Boko Haram ce ta auka
wa masu ibada a cikin massallaci a Falatari da ke
yankin Buni-Yadi da ke karamar hukumar Gujba
a jihar Yobe. Majiyarmu ta labarto cewar harin da ‘yar konar ta
kai wannan massalacin ta auku ne da misalin
karfe 5:30 na safiyar jiya a lokacin da massalatan
ke kokarin gabatar da sallar Asubahi na wannan
ranar, inda tsautsayin ta rutsa da mutane biyu
wadda suka gamu da munanan raunuka, a yayin da ita kuma mai dauke da bom din ta tarwatsa
kanta da kanta har lahira. Wannan dai shi karo na farko da Boko Haram ta
kai hari tun 16 ga watan Afirilun 2016, bayan da
sojoji suka shawo kan wasu matsalolin ‘yan Boko
Haram a wannan yankin. Wadda lamarin ya wakana a kan idanunsu,
Bulama ya shaida wa majiyarmu cewar wata
matashiyar mace dauke da bam din ta nufo cikin
masallacin inda su kuma massallatan suka yi
kokarin tsaida ta daga wannan mummunar aika-
aikar na ta. “Ta tayar da Bom din ne a lokacin da Malam
Yakubu ya tsareta ya yi kokarin hana ta shiga
cikin dandazon jama’a, mai dauke da Bom din ta
mutu nan take, inda shi kuma Malam Yakubu da
Babayo Makanike suka gamu da munanan
raunuka a jikinsu sakamakon fashewar bom din,” in ji Shi. ya ci gaba da bayanin cewar sojojin da suke aiki a
wannan yankin sun hanzarta daukan wadanda
suka gamu da raunukan zuwa asibitin Damaturo
domin samar musu da lafiya da ceto rayuwarsu. Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Abdulmalik
Sunmonu ya tabbatar da wannan harin na ‘yar
kunar bakin waken, ya bayyana cewar wani
mutum ya shaida musu labarin harin da aka kai
“wani mutum ya yi kokarin datse wa wadda ta
dauko bom din hanya domin kada ya barta ta karasa, shi mutumin ya samu raunuka a jikinsa,” Wani mazaunin yankin da lamarin ya auku Malam
Baana Isah ya shaida cewar aukuwa wannan
harin ba zatan ya sanya an rufe kasuwanni,
makarantu, har zuwa lokacin da jama’an tsaro za
su tabbar musu daidaituwar lamarin tsaro a
wannan yankin, gabanin su bude.
©hausaleadership
COMMENTS