Daya daga cikin ma’aikaciyar jinyar dake aiki a sansanin ‘yan gudun hijirar garin Rann ta jihar Borno, Hauwa Mohammed data fada hannun ‘yan ...
Daya daga cikin ma’aikaciyar jinyar dake aiki a
sansanin ‘yan gudun hijirar garin Rann ta jihar
Borno, Hauwa Mohammed data fada hannun ‘yan
Boko Haram a samamen da suka kai sansanin
ranar Alhamis ta sanar da iyayenta ta hanyar
kafar sadarwa Intanet na Whatsapp cewa, su sani fa, ta shiga hannun ‘yan ta’adda. “An kawo mana hari a nan Rann, suna harbi ko
ta ina, dan Allah ku yi mana add’ua, kuma sanar
da iyayena ina cikin matsala!!” Sakon dai an aika da shi ne da harshen Hausa ta
bidiyo, ana iya jin karar harbin bindiga da ihun
mutane a sansanin, in da muryar Hauwa ‘yar
shekara 25 ke kara jadda wa abokananta sako
ga iyayenta na cewa, ‘yan ta’addan Boko Haram
sun yi gaba da ita. Zaka iya jin guje-guje da ihu “An kawo mana hari
a nan Rann, suna harbi ko ta ina, dan Allah a yi
mana addu’a, a gaya wa iyaye na lallai fa ina cikin
matsala, a nemi Fatima ita ma a gaya mata zasu
kwashe mu, ga su nan sun shigo yanzu…” A dai dai wannan lokacin ne a ka ji muryar wani
namiji ya umurce ta da ta yi shiru kada ta sake
motsawa. “Karshen maganar da aka ji daga
Hauwa ke nan, in ji wata kawar ta. Mayakan kungiyar Boko Haram sun kai mamaya
garin Rann ne ta karamar hukumar Kala Balge ta
jihar Borno ranar Alhamis da ya gabata. Bayanai sun nuna cewa kungiyar “International
Committee of Red Cross, ICRC” ce ta dauki Hauwa
aiki na tsawon wata uku don bayar da agaji ga
‘yan gudun hijira a sansanin ‘yan gudun hijira na
garin Rann. Wani abokin Hauwa mai suna Abdulhameed
Algarzali, wanda Editan wata jarida ce a garin
Maiduguri ya ce, Hauwa Mohammed kwararriyar
unguwar zoma ce ‘yar garin Gamboru-Ngala ta
kama aiki ne mako uku da ya gabata, an shirya
zata yi aikin mako biyu a garin Gamboru-Ngala, babbar birnin karamar hukumar Ngala, kuma ta
ziyarce shi lokacin da ta kai ziyara garin
Maiduguri kwana daya kafin a yi garkuwa da ita. Ya ce, wasu ‘yan uwa da abokanan Hauwa sun
dauka cewa, tana aiki ne a garin Gamboru Ngala,
ba garin Rann ba inda ‘yan Boko Haram suka yi
awon gaba da ita. Ya ce, “Daga dukkan alamu bata bayyana cewa
an tura aiki a garin Rann ba, dalilin rashin yi haka
ya daure mana kai, da farko ban yarda da labarin
ba domin Hauwa Mohammed din dana hadu da
ita ta sanar da ni zata garin Gamboru Ngala ne na
tsawon mako biyu, nayi matukar mamakin jin wannan abun ya faru da ita a garin Rann, ina ta
mamakin yadda ta je can” “Zai iya yiwu wa ta ki fada wa mutane in da aka
tura ta ne saboda kada hankali ya tashi
musamman garin yadda garin Rann ya yi kaurin
suna na rashin tsaro, bata son ‘yan uwanta su
hana tafiyar, zai kuma iya zama wadanda suka
dauke ta aiki (International Committee of the Red Cross, ICRC” basu fada mata cikakken inda zata je
domin fara aikin ba, kungiyar ICRC dai na
taimakawa ‘yan gudun hijira fiye da 40,000 a
sansanonin ‘yan gudun hijira na yankin jihar
Borno. Kungiyar ICRC ta bayyana cewa, maikatan ta ‘yan
unuguwar zoma su biyu ne ba a san inda suke ba
tun bayan harin da Boko Haram suka kawo, sai
dai ‘yan uwa da abokanan Hauwa Mojammed sun
tabbtara da cewa, bayan daukan ta aiki da aka yi
an dauke ta a jirgin sama zuwa garin Rann ta karamar hukumar Kala-Balge a jihar Borno ranar
19 ga watan Fabrairu 2018. “Muna ta murnar sabon aikin da ta samu, har
munan mata ba’an cewa, tare da ita zamu kashe
albashin ta na farko in ta dawo Maiduguri” in ji
wata kawarta mai suna Fatima Saeed wadda ita
take nufi a sakon da ta aikia ta WhatsApp. Wasu abokananta sun yi shaidar cewa, Fatima na
da kokarin sadar da zumunci tsakanin abokai da
‘yan uwanta, da farko ma sun yi mamakin yadda
zata iya rayuwa a gari kamar na Rann inda babu
“Serbice” na kafafen sadarwa na waya da
sauransu. Sun kuma kara bayanin cewa, wannan shi ne aikin da ta samu na farko tun da ta
kammala karatu, bayan ta dan yi aiki da kanfanin
Fhi 360 na garin North Carolina ta kasar Amurka
a shekarar in 2017, wannda suka gudanar da
aiki jinkai a jihar Borno. “Amma bayan kwana
biyu da tafiyarta sai na samu sakon WhatsApp daga gare ta, na yi matukar mamaki saboda na
san babu “Network”a garin Rann. “Daga nan ne
ta gaya mani cewa, suna amfani da Internet Wifi
ne a wajen aikin domin aika wa da sakonni da
sadar da zumunci tsakanin su da ‘yan uwa da
abokanan arziki” in ji Misis Saeed. ‘yan ta’addan sun kai hari ne a ranar a dai lokacin
da take tattaunawa da ta WhatsApp chat, sai dai
Fatima ba da Misis Sa’eed ta ke tattaunawa ba,
tana tattaunawa ne da wani aboki can daban
lokacin da ‘yan Boko Haram din suka kawo harin. Duk da wannna tsananin hatsarin da Fatima ke
ciki ta yi kokarin amfani da manhajar WhatsApp
na cikin wayar hannunta a can inda take boye, ta
sanar da halin da take ciki na harin da aka kawo
musu. A cikin sakonin da ta yi kokarin aika wa kafin
‘yan Boko Haram din su gano inda ta boye,
mutum zai iya sawwala yadda a aka kawo harin,
a cikin sakon ta sanar wa abokanan ta a garin
Maiduguri cewa an kawo musu mummumnan
hari kuma sun ruga sansanin sojoji domin kare kan su da kuma tsira daga harin da aka kawo
musu. Amma sakonta na karshe ya nuna cewa, ‘yan
ta’addan sun mamaye sansanin sojoji inda suka
boye kuma a na gab da cutar da ita. Sakon farko
dake tare da karar bindigogi na cewa ne “Inna
lillahi wa inna ilayhi rajium yan Boko Haram sun
mamaye sansaninmu suna neman tafiya da mu” A sako na biyu an ji muryar cikin tsoro na cewa,
“Dan Allah kada ku gaya wa kowa halin yanzu,
kada ku gaya wa Fatima (Muryar cikin kuka) in
iyaye na suka ji wannan labarin hankalinsu zai
tashi, za kuma su yi fushi dani, Wayyo Allah gasu
nan, kuna jin harbe harben da suke yi?” A sako na uku kuwa, kamar ana amsa wata
tambaya ce da aka yi mata a in da take cewa, “Ba
haka bane, suna nan har yanzu kuma zasu tafi da
mu ne”. Ka je ka gaya wa iyaye na ……..ya kuma nuna
kamar an kora ‘yan bindigan ne a karon farko
kafin su hada kansu su kara kawo hari a karo na
biyu, a dan tsakanin ne kuma Hauwa da sauran
abokan aikinta suka bar sansanin zuwa barikin
sojojin domin neman tsira. ‘’Dan Allah, je ka gaya wa iyaye na, su san halin
da ‘yarsu ke ciki ba, dan Allah je ka gaya musu,
ka fada wa Fatima ta je ta gaya wa iyaye na,
amma kada ta gaya musu yanzu yanzun nan” “A
halin yanzu muna cikin barikin sojoji kuma ‘yan
bindigan sun sake dawo wa……. inna lillahi wa inna ilayhi rajiun…” A sako na hudu an ji murya mai tayar da hankali,
in da za a ji muryar mazaje tare da karar bindigogi
dana karafuna, an kuma ji Hauwa Mohammed na
cewa, “gasu nan (“’yan Boko Haram) sun shigo
inda nake, dan Allah kada ka gaya wa kowa
tukunna ina rokonka dan Allah” An fahimci cewa, sako na biyar ya dauki tsawon
dakika biyu ne kacal domin kuwa ya kare ne da
jin ihun Hauwa da ke yi inda take cewa, “Inna
lillahi wa inna…” Sakamakon harin da aka kai sansanin ‘yan
gudun hijiran, kungiyar ICRC ta sanar da janye
ma’aikatan ta masu bayar da agajin gaggawa
daga garin na Rann, sun kuma sha alwashin ba
zasu aika da wasu ma’aikatan ba har sai
gwamnatin tarayya ta samar musu cikakken tsaro, bayan ma’aikatan unguwar zoma guda
biyu da ‘yan ta’addan suka yi garkuwa dasu, an
kuma kashe sojoji hudu da ‘yansanda udu da
kuma ma’aikatan jinya uku a harin da aka kai.
©hausaleadership
COMMENTS