Powered by Blogger.

[Android] Yadda ake gyara matsalar (There was a problem parsing the package) A wayar Android

Assalamu Alaikum barkanku da wannan lokaci, to kamar de yanda na Alkawar ta muku kan cewa zanyi muku bayani na yanda ake gyara matsalar (The...



Assalamu Alaikum barkanku da wannan lokaci, to kamar de yanda na Alkawar ta muku kan cewa zanyi muku bayani na yanda ake gyara matsalar (There was a problem parsing the package) to insha Allah yanzu zamu tsunduma cikin bayani
.
To kamar de yanda kuka sani irin wannan matsalolin suna faruwa a wayoyin android yayin da za,ayi install na wani apps ko games din, wani lokacin sai an turoma da wani apps ko games kokuma kayi download dinsa to da zarar kazo zaka budeshi sai yakiyin install saiya Rubuta (There was a problem parsing the package) kana gani dole saide ka hakura ka gogeshi sakamakon Rashin sanin yanda za,kayi, to idan kunga irin wannan matsalar ya faru to app ko game dinne bana wayarba wato yayi mata kadan kokuma yayi mata girma. Yawancin app din da zakuga hakan to Android minSdk version da targetSdk version din sane baizo dede dana wayar takaba sabi da kowane waya yana tana dauke da nata idan kaga app ya baka wannan matsalar to wannan app din version dinba da bambanci dana wayar taka amma ba version na ainihin wayawa wani version ne mai sune API idan kaga hakan to sune basuzo dedeba shiyasa wannan app ko game yake nuna (There was a problem parsing the package) domin kowace waya da nata API Level din. Sabo da haka insha Allah yanzu zan muku bayanin yanda zaku gyara irin wannan matsalar, abin da ake bukata kawai nutsuwa sabi da haka inde zaka nutsu to Insha Allah zakayi nasara
.
Da farko abin da ake bukata sune:
.
Kuyi Download na "Apk Editor pro" saiku shiga nan domin ku daukota Download apk-editor-pro
.
Sannan kuyi download na "CPU-Z" shima ku danna nan ku dauko Download CPU-Z
.
Kokuma ku daukosu a google kokuma a play store
.
Bayan kun saukar da wadannan applications din to yanzu saikuyi install dinsu
.
Bayan kunyi install to saiku fara bude "CPU-Z" shi wannan application amfaninsa shine bayyana gaskiyar dukkan abubuwan da suka kunshi wayarka kamar model, version, screen size, ram, API Level, da sauran abubuwa da suka shafi kwakwalwar wayarka, to misali idan muka dauki "API Level" to shi wannan shine version na application da zaiyiwa wayarka kuma kowace waya tana da nata "API" to idan kukaga app/game yakiyi yana nuna (There was a problem parsing the package) to wannan API dinne na wayar taka baizo dede dana app din dayaki yiba sabi da haka yanzu bayan kunyi install din CPU-Z din saiku budeshi idan kun bude zakuga Rubutu a sama kamar haka:
.
80, DEVICE. SYSTEM, BATTERY,
da sauransu
.
To kawai saiku shiga "SYSTEM" da zarar kun shiga zai budo muku wani shafi to saiku duba anan xakuga API Level din wayar taku sai kuyi copy dinsa kokuma ince ku haddacesu domin guda biyune kacal zamuzo kansu nan gaba wato zamu gaya muku inda ake amfani dasu


To bayan kun gano API din wayar taku to saiku fito daga cikin wannan app din yanzu saiku koma ku bude "Apk editor pro" idan ya bude ku shiga inda aka Rubuta "Select an Apk File"


idan kun shiga zai kawoku cikin file manager dinku to sai kuje inda wannan app ko game din yake sai kuyi click akansa


da zarar kun danna akansa zakuga ya kawo muku wani Rubutu to saiku shiga inda aka Rubuta "Full Edit (RESOURE RE-BULD)"


Da zarar kun shiga zakuga ya kawoku wani shafi to saiku duba kasa daga gefan dama zakuga inda aka Rubuta "Manifest" to saiku shiga nan


Da zarar kun shiga nan zakuga ya kawoku Manifest na app din zakuga wasu tarkacen Rubutu to wannan tarkacen sune code na app din kowane app ko game yana da wannan domin da sune aka hada kowane irin app/game kuma kowanne nasa dabam. To wannan Rubutun da kuka gani ajere to saiku shiga wanda zaku ganshi kamar haka:
.
< uses-sdk androidminSdkversion ="21" . Ko makamancin hakan,

da zarar kun shiga zai bude muku wani shafi wanda zakuga wasu numbobi misali
.
android minsdkversion
21
.
android tagetsdkversion
22


To wadannan lambobi da kuka gani 21 da 22 sune Minsdk da tagetsdk kowane applicaton ko games yana da nasa lambobin sannan zaku iya ganin wasu lambobin bawai dole sai wanda na bada misalina to idan kunga app/game yakiyi to wannan lambobin sune basuzo dede dana wayar takuba shiyasa app/game din yake Rubuto (There was a problem parsing the package) yayin da kazo install sabi da haka dole sai an chanjasu zuwa na wayar sannan app din zai samu damar yi, kuma kamar yanda na gaya muku kowace waya da nata, idan baku mantaba a farko munyi muku bayanin yanda zaku gano API din naku wanda nace ku gane lambobin zamuzo kansu nan gaba sabo da haka yanzu munzo kansu dan haka wannan API din na wayar taka daka gano sune zaka cire wadanan
.
android minsdkversion
21
.
android tagetsdkversion
22
ka sanyasu wato ka cire 21 da 22 dinnan ka sanya wanda ka gano ta cikin CPU-Z dinnan wato API Level dinnan. Da zarar ka chanja shikkenan saika danna save bayan ka danna zakaga ta dawo dakai shafin to karka damu ka duba sama daga gefan dama zakaga inda aka Rubuta "BUILD" to saika dannan


Da zarar ka danna zakaga ya fara build din saika dan jira kadan har saiya gama da zarar ya gama sai nunama Install da kuma close to sai ka danna Install, nan take zakaga ya farayin install
.
Shikkenan kayi maganin wannan matsalar kuma duk lokacin da irin hakan ya faru sai abi wannan hanyar insha Allah za,ayi nasara
.
Domin karin bayani 08169872309

COMMENTS

Name

Al'ajabi,13,Android zone,69,Applications,3,Aure,25,Blogger zone,1,computer zone,4,Dadin Kowa sabon salo,27,Facebook zone,12,Free Browsing,2,Hausa Films,1,Hausa novels,1,hotuna,2,Java zone,15,Kannywood,55,kiwon lafiya,35,Mata,12,Musics,24,Network,21,News,146,others,16,siyasa,81,Soyayya,3,Symbian zone,5,Video clips,33,video tutorials,3,Whatsapp,1,
ltr
item
Ameer: [Android] Yadda ake gyara matsalar (There was a problem parsing the package) A wayar Android
[Android] Yadda ake gyara matsalar (There was a problem parsing the package) A wayar Android
http://fm.nextwapblog.com/files/6475/01.png
Ameer
https://ameeryau.blogspot.com/2017/12/android-yadda-ake-gyara-matsalar-there.html
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/2017/12/android-yadda-ake-gyara-matsalar-there.html
true
2994989324915487916
UTF-8
Loaded All Posts Not found any posts VIEW ALL Readmore Reply Cancel reply Delete By Home PAGES POSTS View All RECOMMENDED FOR YOU LABEL ARCHIVE SEARCH ALL POSTS Not found any post match with your request Back Home Sunday Monday Tuesday Wednesday Thursday Friday Saturday Sun Mon Tue Wed Thu Fri Sat January February March April May June July August September October November December Jan Feb Mar Apr May Jun Jul Aug Sep Oct Nov Dec just now 1 minute ago $$1$$ minutes ago 1 hour ago $$1$$ hours ago Yesterday $$1$$ days ago $$1$$ weeks ago more than 5 weeks ago Followers Follow THIS PREMIUM CONTENT IS LOCKED STEP 1: Share to a social network STEP 2: Click the link on your social network Copy All Code Select All Code All codes were copied to your clipboard Can not copy the codes / texts, please press [CTRL]+[C] (or CMD+C with Mac) to copy