Powered by Blogger.

[Android] Yadda ake chanja version na wayar Android zuwa kowane irin version darasi na uku (3) yanda ake sanya Custom Recovery

Barkanmu da wannan lokaci, kamar de yanda kuka sani har yanzu muna cikin darasin Yanda ake chanja version na wayar android misali daga versi...



Barkanmu da wannan lokaci, kamar de yanda kuka sani har yanzu muna cikin darasin Yanda ake chanja version na wayar android misali daga version 4.2.2 jelly bean zuwa 5.0 lollipop ko 4.4.2 kitkat zuwa 6.0 mashmallow da sauransu, idan bazaku mantaba mun tsaya a darasi na biyu(2) wato munyi takaitaccen bayani akan muhimmancin chanja version da kuma amfaninsa, sannan munyi bayanin custom Recovery mun fadi ko minene shi, idan baku mantaba munce muku shine uwa uba wajen chanja version, a wancan darasin na biyu mun tsaya akansa, sannan munce a darasi na gaba zamuyi muku bayanin yanda zaku sanyashi a wayoyinku na android,
.
Muna da Custom Recovery masu yawa wanda ake amfani dasu a android to amma a gaskiyar magana nide guda biyu na sani wanda akafi amfani dasu kokuma ince wanda nafi amfani dasu, gasu kamar haka:
.
1-CWM RECOVERY
.
2-TWRP RECOVERY
.
CWM RECOVERY:- shi wannan Recovery cikykykyan sunansa ClockwordMod
Recovery kuma shine Recovery wanda akafi amfani dashi kuma yana da saukin aiki sannan ana amfani dashi ta hanyar madannin volume key up dakuma down sai kuma power on wato madannin kunna waya dasu ake amfani dashi wajen chanja version da sauransu

.
TWRP RECOVERY:- shikuma wannan Recovery din cikyakykyan sunansa shine Team Win Recovery shima ana amfani dashi wajen chanja version da sauran abubuwa sannan shikuma ana amfani dashine da touching wato shi ta6awa akeyi idan zakayi amfani dashi ba kamar Cwm Recovery ba wanda shi da madanne ake amfani shi wannan touch ne.

.
Sabo da haka yanzu zamuyi amfani dana farko wato CWM RECOVERY domin shine wanda yawanci akafi amfani dashi kuma aganina shine wanda yafi sauki sannan nima dashi nake amfani dan haka dashi zamuyi sabo da haka zamuyi bayanin yanda zaka sanyashi akan wayarka ta android
.
Akwai hanyoyi masu yawa wanda ake sanya Cwm Recovery a wayar android, to amma agaskiya magana nide hanyoyi biyu na sani wanda ake sanyashi kuma yawancin mutane da wannan hanyoyin suke amfani sabo da haka nima akan wannan hanyoyin zanyi bayanin hanyoyin sune kamar haka:-
.
1-Ta hanyar amfani da (Rom Manager)
.
2-Ta hanyar amfani da (Mobile uncle Tools)
.
Wannan hanyoyi biyun sune wanda ake sanya Cwm Recovery wanda na sani amma akwai wasu hanyoyin, nide iya wadannan na sani dan hanka zan muku bayanin yanda zakuyi amfani da dukkan hanyoyi biyun dan haka muke zuwa
.
Zamu fara da hanya ta farko wato ta amfani da Rom Manager
.
To da farko kuyi download na Rom Manager.apk zaku iya samunsa a google kokuma play store kokuma kawai ku danna nan ku saukar dashi Download Rom Manager
.
Da zarar kunyi download dinsa sai kuyi install dinsa sannan ku budeshi, amma ku tabbata akwai mb a wayar taku kuma ku bude data, yauwa bayan kun bude wannan Rom manager din to saiku danna inda aka Rubuta (Recovery setup)
.
daga nan zai nuna
muku sunan wayarku saiku danna akai domin ya nemo na wayar taku saiku dan jira kadan zai nemo muku na wayarku to bayan ya nemo sai ku
danna Install (ClockworkMod
Recovery)

daga nan zai fara download na wayarku sanna ya sanya muku shi akan wayar taku, shikkenan kun sanya Cwm Recovery, domin dubawa saiku koma menu na (Rom Manager) saiku shiga Reboot into Recovery zakuga wayar taku ta dauke bayan dan kankanin lokaci saita kawo sannan zata kaiku har zuwa Recovery din da kuka dora shikkenan haka zakuyi wannan itace hanya ta farko kuma itace ake amfani da Rom manager.
.
Ita kuma hanya ta biyu itace wanda ake Amfani da Mobile uncle Tools zaku iya daukota a google kokuma play store kokuma ku shiga nan ku saukar da ita Download Mobile Uncle tools
.
To bayan kayi download dinsa to yanzu sai kaje google ka nemo Cwm Recovery na wayarka kowace waya tana da nata Recovery din kuma zaku samu na kowace waya a google sabo da haka domin dauko na wayarku saikuje google ku Rubuta Download Cwm Recovery.img for sunan wayar taka
.
Misali Download cwm recovery.img for tecno y4 ko makamancin haka
.
Haka zakuyi search a google da zarar kunyi hakan nan take zasu kawo muku shi kala kala saiku za6i na wayarku kuyi download dinsa bashi da wani nawi baya wuce 5mb ko 6mb zuwa sama.
.
To bayan kunyi downlod dinsa saiku ajiyeshi akan memory dinku karku sashi a wata folder ku ajiye kawai akan Memory sannan karkuyi Remane dinsa ku barshi a yanda kukayi download dinsa kuma karku manta ku ajiyeshi akan memory fa.
.
To idan kun gama wannan to yanzu saiku bude Mobile Uncle Tools
idan ka bude zai budoma wani shafi mai Rubutu to saika shiga inda aka Rubuta (Recovy Update)


da zarar ka shiga nan zakaga ya nunoma Cwn Recovery.img din da kayi download dinsa wanda nace ka ajiyeshi akan memory

to da zarar ya nunamashi kawai sai kayi click akansa da zarar kayi click akansa zai nunoma wani Rubutu Are sure flash recovery! To saika danna Ok shikkenan saika dan jira kadan zai doru akan wayarka


da zarar ya gama zai nunama kanaso ka shiga Recovery mode saika danna Yes da zarar ka danna zai kawoka cikin Recovery mode din daka dora, idan kuma ba hakaba to bayan ka gama zaka iya kashe wayar idan ka tashi kunnawa saika danne madannin kunna wayar da kuma wajen kara volume duk a lokaci daya da zarar kayi haka zai shigar dakai Recovery mode din daka dora, idan kuma ka dora din kuma ka shiga sai kaga Ya rubutoma no Comman Found to karka damu wanna cwm recovery.img dinne daka dauko a google shine bamai kyauba. To karka damu sai kayi hakuri ka koma google din ka dauko wani sai kazo ka sake gwadawa insha Allah zaka dace
.
Wannan sune hanyoyin da akebi domin dora cwm recovery a wayar android
.
Da fatan kun gane wannan darasin
.
Idan kuna da tambaya ko neman karin bayani saiku ajiye comment kokuma ku kiramu a wannan number 08169872309

COMMENTS

Name

Al'ajabi,13,Android zone,69,Applications,3,Aure,25,Blogger zone,1,computer zone,4,Dadin Kowa sabon salo,27,Facebook zone,12,Free Browsing,2,Hausa Films,1,Hausa novels,1,hotuna,2,Java zone,15,Kannywood,55,kiwon lafiya,35,Mata,12,Musics,24,Network,21,News,146,others,16,siyasa,81,Soyayya,3,Symbian zone,5,Video clips,33,video tutorials,3,Whatsapp,1,
ltr
item
Ameer: [Android] Yadda ake chanja version na wayar Android zuwa kowane irin version darasi na uku (3) yanda ake sanya Custom Recovery
[Android] Yadda ake chanja version na wayar Android zuwa kowane irin version darasi na uku (3) yanda ake sanya Custom Recovery
http://fm.nextwapblog.com/files/6475/clockworkmod-recovery.jpg
Ameer
https://ameeryau.blogspot.com/2017/12/android-yadda-ake-chanja-version-na_20.html
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/2017/12/android-yadda-ake-chanja-version-na_20.html
true
2994989324915487916
UTF-8
Loaded All Posts Not found any posts VIEW ALL Readmore Reply Cancel reply Delete By Home PAGES POSTS View All RECOMMENDED FOR YOU LABEL ARCHIVE SEARCH ALL POSTS Not found any post match with your request Back Home Sunday Monday Tuesday Wednesday Thursday Friday Saturday Sun Mon Tue Wed Thu Fri Sat January February March April May June July August September October November December Jan Feb Mar Apr May Jun Jul Aug Sep Oct Nov Dec just now 1 minute ago $$1$$ minutes ago 1 hour ago $$1$$ hours ago Yesterday $$1$$ days ago $$1$$ weeks ago more than 5 weeks ago Followers Follow THIS PREMIUM CONTENT IS LOCKED STEP 1: Share to a social network STEP 2: Click the link on your social network Copy All Code Select All Code All codes were copied to your clipboard Can not copy the codes / texts, please press [CTRL]+[C] (or CMD+C with Mac) to copy