Blog Archive

Powered by Blogger.

[Hausa novels] DOWNLOAD NIDA KISHIYATA COMPLATE

saukar da wannan littafi mai suna Ni da kishiyata domin nishadantar daku, saiku danna nan DOWNLOAD domin saukar dashi akan wayoyinku na And...



saukar da wannan littafi mai suna Ni da kishiyata domin nishadantar daku,
saiku danna nan DOWNLOAD domin saukar dashi akan wayoyinku na Android, java, symbian, da sauransu
.
Kokuma ku karantashi anan.
.
NIDA KISHIYATA COMPLETE


==>NIDA KISHIYATA 1 ==>Kallo daya tak namata najuya kai domin ji nake kaman nayi amai. Lalle haidar yayi kokari.ko meya gani ajikinta yakeso?! Wata xuciyata tace farin yagani. Tsaki kuwa naja.to ai kuwa dawannan farin gwara wata bakar goma.magananta ne ya katseni kitashi kidaura abincin don yau banajin zan iya yi.ko kallanta banyiba.tamaimaimata yakai baki goma sannan nace kina cika min kunne!! Dawa kike magana nekam?! Jafar uba!! Lalle shatu kin rainani.naja tsaki nace kin dai yi asara ladi kike kome?! Ran girkin kinne zakice namiki girki?! bayan kinci kwaliyya abinki kina jira miji yaxo.wato ke mai miji.beta ki kama kanki.tayi tsugut tana kallona. Na zare ido sosai sannan nace nidince dai aishatu bawataba kinsamin ido kaman zaki cinyeni.batace komaiba taja tafice. Nima sainamike ina tunanin yadda haidar ya kwasomin wannan shiririnta wai kishiya! Sunana aishatu usman kado.mubiyu ne kawai agun iyayena dani da twin brother na wato aslam.muntaso cikin gatan iyaye don momy nah tagayamin cewa saidasukayi shekara takwas Allah yabasu haihuwa.sunyi yawon har sungaji. Dayatashi basu saiya basu mubiyu.kuma tunda lokacin baikara basuba. Hakan yasa suka dauki kaunar duniya suka dauramana. Musamman ni mace. Mahaifina yanada arxiki sosai gydaje da motocci yake sayarwa.haka yanada jirage nakansa. Karatunama a turkey nayi tundaga grade 1. Har uni. Nayi grad.tukun naxo naija nayi bautan kasana. Nakamalla komai inada shekara 23. Anma ga duk wanda zaiganni zaidauka shekarana 17 ne. Inada karamin fuska .nakaranta business admin.a skul.dadyna shuwan maidugurine .momy kuma fulanin yola. Hakan yahada yabani kyakyawwan zati da kira da Allah yaban .ni doguwace.jikina irin kiran kalangu.wasu kuma kance coca cola shape.inada yoloyolo gashi wanda yasauka min har gadon baya baki kirin. Gakuma wani wanda yarufamin gaban fuskana. Inada dogon fuska da tsuakken bakinanandaidai wanda karan hancina ya xubo yayi daidai .dimple din fuskana sai tubarkallah. Gakuma dara daran idanu wanda idan kacire dogon fuskana mutane suna cewa sak kammanina da ashwariya musamman ido. Wani irin ido nakedashi wanda nikaina tsoron kallon mutane nake. Musamman maza . Don bana mantawa nasha samun matsala da maza akan idona .wata rana a makaranta nayi lattin lectures. Dasauri nadoshi ajin ina xuwa naga anyi nisa sosai. Don haka sumi sumi nasakai zanwuce saikuma lec. Din ya tsayar dani.kaina akasa yace meya tsayar dani? Nace am sorry sir! Yahau banbani da matsifa ido nadaga kawai ina kallonsa yanata matsufa yana xuba chemicals din dayake practical kawai muka hada ido. Nima kallonsa nake. Kara mukaji wata tayi yasa nayi firgit najuya don ganinme ashe shine yake kwaba. Yana diluting chemicals yaje yajuye ajikin rigansa baisaniba.kaf kwalvan suka fado duk baisaniba. Saidaga baya yake rike goshi bayan yaga kwaben dayayi.nikuwa hakan yabani daman shigewa aji. Yan aji kuwa suka fara dariya.ahaka ya tunxura sosai. Tsawa yabugamin. Tsumi tsumi nafito yanuna min hanyan waje haka kuwa nafita. Wayata ce aka bugo .donhaka dasauri nadauka don nayi zaton course mate ditace Maryam maleka. Saikuma naga megidan ne guda na gyra murya na sosai.sannan nadauka . Hellooo babynah! Yace naam dear yakike? Lao wlh. Nayi missing dinka. Kibari kawai. Me kika girka min yau?. Nayi kwasaf sannan nace dear kamanta yau matarka ce da girki baniba?.yace na mantane. But kimin alfarma don Allah kitashi kidaura min . Dasauri namike. Nace to badamuwa kakula min dakanka tak kia. Da sauri na nufi kicin nafara tunanin mezan daura masa mafi sauki?. Bari dai namasa jollof din taliya da tsiren kifi . Bayan na kammala. Nadan rage gas din dan ruwan yashanya komaina daidai nanufi daki nakara wanka naci kwaliyya. Naxo na kwashe abincin na juye masa a kula. Na gyra dakin tsaf. Na feshe da turaren wuta. Sannan na harde kafa inajiran maigidan. Karan horn dinsa naji donhaka dasauri namike naje na tarbosa. Rungumanshi nayi. Na sumbaceshi kamshin jikina daya shaka yasashi jan wani irin numfashi. Nakarbi brief case din. Najawo hannunshi mukayi falo sannan nacire mar takalmi mukaje nakaishi yayi wanka nabashi kaya yasaka sannan yafito da xummar cin abinci. Na gyra zama na harde. Inajira yafara santin daya saba idan namishi abinci. Loman farko ya tsuke fuska. Hakan yasa nace yau kuma tahaka zakayi santinka? Yatofar a gefe. Habawa nanfa yafara matsifa. Aishatu ke wacce irin macece. Don kinsan banacin gishiri shine wato bari ki lapta namutu ko?. Na zaro ido. Nace wlh dear daidai nasa. Cokalin yasa yacuso min a baki nahadiya don dole wani irin yunkuri nayi aikuwa yadanneni billahilaxi saikin cinye. Wato ki kasheni kimin asaran kudin gishiri


==>NIDA KISHIYATA 2 ==>Na marairaice haba babynah yazakana haka . Wallahy ko dana kusan karasawa saidana dandana komai yayi daidai. Ya harareni sannan yace gishirinne yake miki hassada dayaga kingama yaje yashiga abincin. Banca komaiba haka yakaraci matsifansa .dama haka haidar yake xuciyar kamar me. Yanxu yanxu sai yahau yarikice wa mutum karasa inda zaka tusashi don lallami anma sai yakai aya tukun zai barka. Bayayan yafice nadau abincin nakai kitchen nadawo na kimtsa gun . Anan naji karar mota alaman wato zaifita yanafita ban nufi ko inaba sai dakin lami. Na kalleta nace ke wai haifanki akayi da makirci?. Tayi murmushi tace wanda ya iya allonsa yawanke!. Nace haka kikace? To wallahy muxuba!.zakisan shiga hancin shatuu ba abune mai saukiba.gyra kafa naga tayi axatona tashi zatayi saikuma naga tayi wani irin zama ta karkace tasake wata kakkauran tusa. Ga uban kara ga uban wari. Hanci natoshe nafita dagudu tabini dawani baxawarar dariya. A dakina kuwa shawarar yadda zan rama nake. Ni ba gwanan makirci ba anma tunda haka ta zaba muxuba! Can nayi wani irin murmushi sannan namike Lami dai matar haidar ce tafarko maana nashigo na sameta. Nayi mamakin rayuwan dasukeyi don zan iya cewa zaman hakuri yake da ita. Kodai yane akwai dalilin kin sakinta anma da yanda nasan haidar wlh daya dade da tunkudata kgydansu. Fara ce sosai.tanada dan jiki. Kananun ido irin na yan china don nafi kwatanta dasu. Batada tsawo tanada gashi. China dai sak. Lami irin matan nanne masu son jiki. Basu tsaftace muhallinsu. Hakan yasa kazanta ya bakunci rayuwanta. Ga dan banzan kuiya. Tafiso taci takoshi .ta kwanta. Wato dai ci da sha. Tusa da kwanciya. Kullum acikin rikici suke da haidar. Kuma koya zasuyi yana idda mata matsifa zata mike tayi baccinta. Batq gyra kuskurenta. Bai dameta su shirya .ko su bataba. Yanuwanta ne dai basu yi wasa da gyrata ba maana gyran mace bisa ga maganij mata. Wannan kadai yake taimakonta maigidanta yake ganinta da gashin ido. Xuwana gydan komai yacanja domin kuwa idan har yasan bazatamishiba toni yake sawa. Hakan yasa wataran nake mata gorin abun kozatayi xuciya anma inaaa kare ya lashe xuciyan. Ni dai bansan ana cutan tusaba. Anma nakanyi mamaki sosai akan lami. Ko magana kamata wanda bai gamshetaba zata karkace ne ta bunka maka tusa. Mai warin tsiya. Cikina yasha kumbura akan tusanta. Anma naga ita ko ajikinta. Bai damentaba. Bamu dai taba magana mai zafi da itaba. Don ita macece marar son magana. Hayaniya baya damunta. She speaks loud in makirci. Anma a zahiri innocent. Ta iya hada kananun tsibbu. Donkuwa hakan yasa danaga gishiri yayi yawa nasan aikin tane. Kuma koda kuwa aikine maifida yasa batayi niyyanyiba. Kuma naga tana complain to nasan akwai matsala don ahankali saita bata zance. Bansamu nashawo kan maigidanba saidaya dawo kaina kwana. Ranan na lallabi abuna muka shirya. A daren yake cemin gobe abokai na zasuxo dinner. Donhaka keda lami zakuyi mana girki sosai. Nace insha Allah babynah. Washegari dasafe na dudduba abinda muke bukata a kicin narubuta driver yasiyo mana. Tun karfe 2 nafara hade hade. Lami kuwa taxo tazauna akan kujera da earpiece dinta tana dan tayani wani abun can taja wani tsaki nace meye kuma Lami kanu??? Tace wannan wani iskancine abokanshin basu da gyda da mataye ne?. Nace don yau zasuxo cin abinci gydanki?. Tace ai aikin wahala ne. Nifa baxan iyaba nace ke kikasan wannan ol i kne shine kixuba tsamayen hannunki mu karasa. Tayi shiru. Tsimi tsimi kamar abun arxiki harta fara yi. Saikuma tamike . Ke shatu agama lafiya tafice. A zuciyana nace wayyooo Allah dukka aikin nan nizanyi?.wayata nadauka nakira mai aikinmu cikin minti talatin taxo mukayi aiki chap muka gama najera musu a falon maigidan. Na sallami mai aiki naje dakin lami. Nayi murmushi sannan nace lami don Allah kidubi girman Allah karkisa komai a abincin nan. Baki nefa. Ta kallen batace komaiva. Nima najuya anma nagagara yadda da ita. Tunda tanada acess da dakin. Addua nayi nawuce . Bayan na kimtsa nayi sallan magrib nayi na isha . Ina addoi naji shigowansu. Nazauna nagama tukun namike cikin farha na tarbesu muka gaysa sannan nace musu . Ga abincinsu na tashi nafice. Naxo karamin falo.. sunaci suna santi naji dadin hakan sai yabonmu suke a tunaninsu mubiyu mukayi. Lami nagani zata wuce na kalleta ban ce komaiva tasa kai. Bayan sungaisa kaman abin arxiki. Nidai hankalina ya gagara kwanciya. Aiko bangama tunani ba. Naji wani irin kara. Bakomai bane illa karan tusanta. Bashiri naga suna rige rigen fitowa


==>NIDA KISHIYATA 3 ==>Bayan sunfitone kowa toshe da hanci. Haidar yace na kwaso musu abincinsu zasu zauna anan falon .nadaura gele na ta hanci bayan na kwaso musu lokacin kuwa lami tayi dakinta. Nabita rike da kugu haba lami yanxu abin kunyan nan har ina?. Ai wannan gwara ki xuba gishiri akan kiyi tusa. Kinxubar da mutuncinki dana mijinki!. Ta kallen ta gefen ido . Ke shatu angayamiki da gangan ne?. Mantawa nayi . Nace owwwwh kinma san lokutan dakikeyi kenan? . Kaman bazata amsaba anma sai tace. Duk lokacin danayi wani irim zama to sai nayi tusa. Nace to keda kuke tare da abokan miki meya kaiki wani zama. Kee shatu kindamen. Nace very gud. Nafice raina yabaci.abin takaicima sun gagara karasa abincin. Haidar kuwa kaman ya hadiye rai yamutu. Suna tafiya ya fizgo kunmenta. Wani irin rashin mutunci ne? Yazaayi kimim tusa agaban aboksi? Wanda kike min bai ishekiba?. Nanfa yafara matsifa. Kuka tafarayi har saidataban tausayi. Nace ba laifinta bane. Kamata yayi kanema mata magani. Baice komai ba yawuce daki. Ranan ban gane kanshiba. Donhaka najuya naci baccina. Nanma ashe na tsokana jafai da safe yarinka mita wai wato ban damu dashi bane shiyasa nayi bacci .dakyar na lallabesa yafita aiki. $**Gamawana makaranta yasa nafara aiki a gun baba. Inadan managing masa wasu abubuwa. Watarana nafito gyda nanufi grand square. Inaduba chocolates don Allah yadauramin sonsu . Bugewa nayi da abu dasauri nadago donganin meye fuskarsa nagani . Baimin kama da dan nja ba. Anma kana ganinsa kasan danhutu ne. Fuskar tausayi nayi nace am so sorry. Yayi murmushi .bakomai so aw yu doin?. Na karkace kai na kwashi abubuwan danake bukata sai dana bar layin butcheries din sannan nace m fyn. Saiyayita bina. Bayan nabiya matan taje anriga anbiyamin nace tarike kudin bannaso. Motata nashiga nadau hanyan gyda. Alokacin na lura cewa yana bina. Saidanaxo daidai gyda nasauka. Yafito shima batare da najira yace komaiba nace nagode da rakiya. Kwana uku a tsakani. Momy takirani wai naxo abokin dadyy yabani danshi. Na kalleta nace nikuwa ace masa nagode bana so. Tace aikuwa kinsan karya kenan. Mutumin daya taimaki dadyn ki lokacij da dadynki bai dashi?. Aiko shi zai aureki rsaf zaabashi balle dansa. Najinjina kai . Ganin dagaske take. Nace momy inbana sonsa fa koshi baya sona. Tace to ai yaron shi yaganki yakeso. Bance komai ba jikina yayi sanyi duk son da iyayena suke mim sunmij tarbiyar amincewa wa duk wani bukatarsu agareni. Ahaka muka hadu naga ashe haidar ne wanda muka hadu a grandsquarr. Munyi soyayya mai karfi. Bai taba gayamin yanada mataba saida aka sa ranarmu. Nan munyi rikici sosai kafin nayadda. Na aureshi $**** Nashiga dakinsa na kimtsa kayansa. Nawanke masa inners. Naje nadora girki. Bayan sunbushe nagoge. Nafeshe dakin da turare narufo sannan naje wanka. Bayan nafito nashirya tsaf. Ina mikewa naji karar motansa da gudu nah tarbesa. Munshigo falo kenan. Saiga lami tashigo. Shatu ana magana dake a waya. Nace kowaye yajira nasallami mijina. Sai tace mamanki ne. Namike nace baby jirani naxo nakaika wanka. Naje nadauki wayan mama muka gaysa . Tace lafiya kika kirani?.nace nikuma mama? Tace ae. Nace ae nakira ne mugaysa tace tom sai anjima. Acigaba da biyayya. Nace to. Na ajiye wayan ina tunani. Nidai nasan bankirataba. Ban idda ba naji haydar na kwalamin kira cikin fushi. Nan gabana yafadi toh hajiya lami kanu!!!!!! Mekika kulla mun?ina isa dakin mari naji a fuskana nadago zanyi magana yakara watsomin na biyu. Dasauri narike kuncina. Mena maka? Ya kallen cikin tsana. To Allah yakamaki. Wato shiyasa kikace najiraki ko?. Aisha yaushe kika fara asiri?.wannan magungunan me? Naga hannunsa . Maganine wanda bansan ya akayiba. Ansasu a gefen ruwan wankanshi. Sauran kuma a gefen pillownshi .inaga yaxo ajiye wayansa ne yagani. Nace wlh bansandashiba. Kimin shiru . Nan lami tashigo tana yatsina fuska lafiya swtat? Yace inafa lafiya. Tafara bin malamai .cikin tsorata tace shatu??!. Yace banda lokacinta. Mamanta zankira susan me ake ciki.yana fita takallen tace Kenan mai miji ko?. Gwara dukkanmu kar azauna lafiya. Tajuya tatafi. Takaici bai ishenba saidanaji haidar na xukawa momy nakarya. Wlh momy magani abayangida anrubuta mallakan miji!!!!


==>NIDA KISHIYATA 4 ==>Haushi ne? Kuka ne? Dariya ne? Narasa wanda zanyi. Lallaima wuyan haidar yarika. Har yanada bakin kiran mahaifiyata yamin kazafi?. Dakina na nufa nafara tattara kayana ina gamawa naja akwatina na fito. Dasauri lami taxo haba dan Allah shatu. Ina zaki?. Hannu nasa mata nace keee hold on to it.!!banson rainin hankali kinsan abunda kika aikata wallah ina horonki da kiji tsoron Allah. In mijiine kuma. Gaki gashi ki cinye nabarki dashi. Tana cafko akwatina wai ita adole ta gwada masa ita mai tausayine. Na buge hannunta nafice. Ina xuwa gyda momy takallen cikin zafin rai. Mekikaxomin agyda? Ko kinxo mallakana ne nima? Nadan saduda kai nace momy ki yadda dani. Wallah bansan kome ba. Takallen tace mijinki zaimiki karyane? Ta taso zata kwadeni. Na sunkuyar dakai sai naji shiru kuma. Hannunta nagani daddy yarike. Lafiyanki kuwa? Meta miki zaki daketa?. Tamayar masa da abinda haidar yafada mata. Yaja tsaki yace ke kuma sai bakisan tarbiyar dakikayiwa yarkiba? A a alhaji yaron yanxu baa shaidansa. Bawani. Zonan aisha kimayarmin meya faru. Nan namusu bayani. Saa na daya momy ta yadda. Acematan danayi ni bankirataba akacemin takira. Tace to ai taga missed call ne . Nanfa ta yadda . Daddy yace saikiyi hakuri kikoma. Momy kam takafe ba inda zanje. Sai yaxo baiko tukun. Acuceni ahanani kuka? Wannan bamaiyiwuwa bane. Bayanda daddy baiyiba momy takafe tace sam batasan zancen ba.aikuwa dole nazauna. Wasa wasa har nakai wata ba haidar ba labarinsa.abun yafara damuna nidai nasan ba zaman arxiki sukeba. To meya hanashi xuwa? Kodaman basona yakeba?. Momy talura dahakan yasa tayi magana wa daddy incigaba da aiki. Yace sam ai akwai auren wani akains. Da izinin wa zanje ko kofar gyda yahanani xuwa wai inada miji baimin ixinin fitaba. Dole muka hakura nida momy .natashi dasafe nayi brush naxo dinning doncin abinci. Kamshin kwan danaci shiyasani tashin xuciya. Nanfa nafara amai kamar zan amar da kayan cikina. Shine momy tajani muka je asibiti anan likita yace inada ciki wata hudu. Nayi murna araina .afuska kuwa na damke. Munje gyda bayan angayawa daddy yace to yakamata asanar dashi yasan da cikinsa. Sannan asan matsayin zamana. Yakirashi yace yaxo gyda yana nemanshi. Xuwanshi ina kwance a karamin falo ina kallo. Anma jin muryarsa yasa nadan rufe ido saboda yayi tunanin bacci nake. Bayan yashigo ne yakaremin kallo sannan yawuce nikuma nabishi da harara. Anan sukayi magana da daddy yacewa daddy shibaisan nafitoba. Bangayamasa ba. Nan daddy yamasa maganan cikina. Dakuma zama ko ya sauwake. Nanfa yace a a daddy takoma kawai. Daddy yace to kaje kadauketa kuwuce yanxu . Momy nakira nagayawa abinda daddy yace tace aina akataba haka?. Yabarki zankaiki anjima. Anma ina daddy korani yayi. Muna shiga gydan toshe hanci nafarayi domin wani irin hamami naji . Muna shiga site dina naga tabargasa donkuwa ba abunda baa caje adakinva. Nace mekaxomin adaki yakallen sannan yace bani bane. Nankuwa axuciyana na ce. Dole nayi maganin lami koda kuwa zanmutu wannan wani irin iskanci ne?. Nasauke kayana na kimtsa dakin inayi inahutawa.a zuciyana nace inama shegiyae tke? Bara nadubota. Dakin gam najishi axuciyana nace ta tafi yawontan nan. Yawon tsiya kaman me. Kullum tana gydan kawaye.shikuwa kaman soko baya hanata. Nakoma nagyra gidan tsaf. Nadaura indomie naci nakoshi nayi tam. Namike kafafu . Sallama naji yashigo da ledodi yana wage baki. Ko kallonsa banyiba. Dayagaji da zama yace ina abincina?. Nace ina matarka?.shiru yayi. Can yamike yafice. Sallah nayi. Najira isha bayan nayi .nakashe wutan dakina anma ban rufe kofanba acikin bacci naji ana tabani. Juyowa nayi naga mutum akwance agefena. Naja tsaki nace mekakemin a daki?. Baice komaiba. Donhaka na bangajeshi na juya nacigaba da baccina. Hasken wutan dakin aka kunna. Cikin matsifa najuya ina cewa. Wani irij iskanci ne mutane suna kwance zaka kunna musu!!!@@ cak na tsaya don wanda nagani na tsorata. Haidar ne a tsaye. Gakuma wani a kwance ba riga agefena


==>NIDA KISHIYATA 5 ==>innalilahy wainna ilaihi rajiun nake fada . Yayinda na gefen nawa wanda bantaba ganiba ya mike daga shi sai gajeren wando. Yatattari kayansa a hanzarce yafice a dakin. Haidar kuwa zan iya cewa mutuwar tsaye yayi.nikuwa bantaba tsinta tashin hankaki ko na ganshi kaman na yauba. Mezance? Ga hujja baro baro ankamani. Kuka nasaka mai karfi wanda numfashina saidaya dauke. Farkawa naganni a asibiti tare da momy. Tana ta xubda hawaye. Numfashin danaja su suka tabbatar mata dana tashi. Juyowa takallen cikin zafin rai. Matsifa ne a idonta anma hada ido dani yasa tayi sanyi sosai sakamakon yanayin data ganni aciki. Yajikin dai? Na gyada mata kai sannan tajuya. Minti goma a tsakani saiga daddy yashigo. Nanfa yarufem da fada. Aisha idan baki kiyayeni ba zan yafeki . Kuka ne yaci raina sorry. Aslam ne yashigo. Ganin halin danake ciki yasa yarude. Sis meyafaru? Meya sameki? Waya tabaki? . Daddy ne ya janyeshi. Yanxu kadawo daga makaranta kaje kaci abinci kahuta tukun. Ya kalli daddy cikin bacin rai. Yace wato tun tafiya na kuka sata agaba ko? Shikenan daddy duk abinda yasami yaruwata kune sanadi. Dasauri yafice.daddy kuwa harya harxuka anma momy tace karka ga laifin shi. Laifinka ne. Wayace katurashi waje karatu? Gashi yakwaso aladansu ai. Daddy yafice banko kofan yayi dakarfi. Wanda saidana rufe idona. Abunda yafarune yake dawomin cikin ido. Allah ya isa tsakanina dake lami. Abunda naketa fada kenan. Momy ne tace me lami tamiki? Kome kice lami? Baa taba jin kansuba saike!. Girgiza kai nayi nace momy bazaku gane ba. Dama yaushe zangane? Inada kwalkwalwan kifi? Lamin nan ladabi da biyayya. Koda aka kawoki asibitin nan yarinyan nan sau uku tana xuwa duk tabi ta damu. Wani murmushi wanda yafi kuka ciwo nayi. Nace lami din kenan. Kedai yanxu bakida bakin magana. Na sadda kai. Ahaka har likitan yazo yaduban . Yace jinina ne yahau. Donhaka aguji batamun rai dadai sauran shawarwari.


==>NIDA KISHIYATA 6 ==>wata rana natashi da nakuda atake aka kaini asibiti. Nan nahaifo santalelen dana. Wanda dashi da ubansa sak. Nanfa akafara sanar da dangi da yanuwa. Muna shirin tafiya gyda saiga lami da wata kawarts Ko kallo basu ishenba. Dama dan nawurin goggo. Donhaka tamika musu.nan sukasa albarka harsuka tafi ban ce uffanva.nanfa su momy suka fara min fada. Wai kishine ke damuna. Nace Allah ya sauwaka. Mezaisa nayi kishinta?. Bayan munje gyda nan yanuwa suka fara tururuwa . Harda aslam da matansa. Da dai abokan arxiki. Ran suna da yaci sunan kakansa wato babana usman. Muna cemasa abulkhair. Son dana ne yashiga raina sosai. Ina tattalin abuna. Tunda nahaifi abulkair gashi ina neman wata hudu. Haidar baitaba kira yajiba. Baitaba xuwaba. Balle yasan yana da da.komai ni da iyayena mukeyi. Alokacin dana yayeshi a wata goma sha daya nan nafara fita aiki. Wata rana nafito aiki mota na ta tsayamin akan hanya. Narasa yadda zanyi. Gashi titin motoci daidai ne. Nanfa naxauna ga rana yayi zafi. Can wata mota taxo tatsaya ban dago naga wayeba. Sallama naji donhalka na daga kai tare da amsawa. Dogone yanada matsakaycin jiki. Inka ganshi zaikai irin 42. Fari sol. Daga gani inba fulani ba to yanada alaka dasu. Duk wannan namasa a kallo daya da musulunci ta hallata ne. Najuya kai.sannan yace lafiya naganki haka? Nace wallahy motanne is at fault. Yaje yadan dudduba. Sai yace y not kishiga motana muje inkaiki gida. Sai inkira aduba. Yanxu kafin aduba dare zaiyi kuma kinga ke macece bai dacebs. Nadanyi jim. Sannan nace a a kabarshi kawai. Yace haba yanmata. Dasauri najuya nakalleshi gira yadagamin alamum he meant wat he said. A xuciyana nace bakasan har kwai na ajiyeba. Kana wani cewa yanmata. Yace shiga muje mana plxxxx. Yadan marairaice kaman karamin yaro.hakadai nashiga nan nagayamasa gydanmu. Yana tafiya yana jana da hira ina amsawa sama sama.don ban sake dashiba.mun isa maigadi yaleko kansa dayaga inaciki sai yabude kofan. Bayan munshiga ne nayi godiya sannan nafito. Ina shiga naga abulkhair sai wangale baki yake. Nanfa nadaukeshi mukayi daki. Kwana biyu a tsakani akace ana sallama dani. Nanfa nayi mamaki sosai. Waye haka da kokari. Fitana keda wuya naga ashe shine. Muka shigo nakaishi falon baki. Muka gaysa namishi tarba na mutunci . Anan yake cemin sunanshi suleiman. Yana da mata daya da yaya biyu. Shi yana sonane kuma da aure. A lokacin abulkair yashigo yana tatata. Namike nadaukeshi. Ya kallen yace fyn boi. Dan waye haka. Nayi murmushi sannan nace dana ne! Bude baki yayi ban yaddaba. Nace wlh. Yayita mamaki yana cewa wallahy ko kama da matan aure banyiba. Inyi hakuri. Nace ae ba auren ne yanxu. Nanfa yayita mamaki wai wlh i look very young. Nandai muka danyi tadi .bayan tafiyansa ne. Wayata yayi ringing naduba naga bansan numbernba. Nakuwa dauka. Kudi yaboyeki abinda aka fada kenan. Nan nayi murmushi dan kuwa nagano muryar waye. Wata runaway frnd dinane Benaxir omar. Nace kina nan kuwa? Tace inanan yakike yahaidar? Nayi murmushi nace kina ina? Tace jiya nashigo gari. Nace kixo gyda gobe akwai magana tace to. Nan ta kashe wayan. Murmushi nayi donkuwa nasan kawartawa. Zata magancemin komai. Dare dare muna zauna saiga daddy yashigo. Kufito falo ina nemanku. Nida momy muka mike mukabi sawunsa. Gabana ne yafadi ganin haidar dakuma wani. Wanda nakega kaman nataba ganinshi awani guri anma namanta ainane. Daure fuska nayi sosai bayan nanemi guri nazauna ne. Daddy yafara magana. Aisha mijinki ne yaxo mana dawani babban alamari. Shine nace barin kiraki kiji dakunnenki. Nan yafara magana. Daddy nayi kuskure na rashin fahimtan aisha. Na zalunceta sosai don naga tanamun biyayya anma ba laifina bane. Wannan mutumin shine wanda nakama shi da aishatu tun ranan bankara ganinsa ba sai daxu akan hanya. Ana rikici dashi akan kudi. To banganeshiba donhaka ma naje nakarba masa fadan. Nabiya kudin da ake binsan. Harzantafi sai yace yaganeni gyda kaza ko,? Nace masa ae . Sai yace to tabbas zaigayamin gaskiya don nataimakeshi bazai cucenba. Nan yake cemin akan nataba kama matana dawani?to shine. Kuma shima turoshi akayi. Anma yarantse min babu abinda yashiga tsakaninsu. Yace min lami ne taturashi tasashi aikin. Nan fa jikina yafara bari namike. Nace kagani ko? Ina ba abunda kamun? Bansan kaibane? Wannan tambayan najerosu ne lokaci guda. Atake kuma nafadi


==>NIDA KISHIYATA 7 ==>Farfadowana sakamakon ruwan dasuka kwaramin naja numfashi sosai sannan lumshe ido. Ina mai tuna abinda yafaru. Momy ce ta tarboni natashi. Hawaye ne sosai a idon haidar. Yana rungume da abulkhair. Dasauri nace mikomin dana. Meye haka kawani damke shi . Momy ce tamin ido donhaka nayi shiru. Nan haidar yacigaba da bayaninsa. Bayan nakoma gyda zanyiwa lamin tsiya naci karo da ita da kawayenta su hudu suna mashaa adaki (lesbianism).abun ba dadinji bayan nabata takardan saki. Naje dakinta zandibi kayana naga kullin magunguna da layoyi. Yanxu wallahy nayi nadama. Don Allah abba kuyi hakuri. Abba dai waaxi yayi tamasa. Dangane da yanke hukunci cikin gaggawa baikamata kayi hukunci cikin rashin saniba.aikin shaidan ne. Sannan kai kake zaune da matanka. Kaikuma kasansu. Kasan abinda zatayi da abinda bazatayiba. Abba yamasa nasiha sosai sannan akarshe yace yaje yaneman mu sasanta idan na yadda to. Idan ban yadda ba shikenan. Don bazaimin doleba.nan shida momy suka fice. Naje na kinkima dana nabarshi agun.yana kiran sunana .banyi baccin dadiba ranan.tunani burjuk araina. Washegari nashirya tsaf ina jiran aminiyan tawa benaxir. Karfe biyu daidai saigata Namike natarbeta ina murna. Yauwa yar albarka.sannunki. bayan munci munsha. Namata bayanin komai. Tumdaga zamanmu da lami har matsa inmu. Takuwa jinjina kai lalle sannunki. Ai bahaka akeba. Ai idan kina zaune da kishiya tamiki abu to shareta zakiyi. Tunda bata nemi zaman lafiya ba. Ki koma gun mijinki. Shi zakina lallabawa kina tarairaya. Karki bari wani makircinta yayi tasiri akanki.nan na jinjina kai. Nace ai haidar xuciya yake dashi kamar me. Baya saurare tace. To keba mace bace? Ke hoto ce? Da niiman da Allah yabaki zaki jawo mijinki gareki. Nanfa ta cire gyale tafara hidima. Ta gyrani sosai. Tundaga jiki. Har abunci dasha wanda zan gyru ciki da bai. Sannan tace inta nine inabaki shawaran ki koma gydan mijinki. Anma fa bawai yqnxu ki aminceba. Kudan ja aji. Tunda kema anmiki. Dole abiki yanxu. Har dare muka kai muna abu daya lalle gyra kam sai tubarkallah. Anan sulemanu yakiran mundanyi waya kadan. Haidar kuwa 13missed calls.


==>NIDA KISHIYATA 8 ==>Anma ko dauka banyiba hakan yasa ya jeromin txt. Dahar zan goge sai kuma na tsinci kaina dason karantawa. Dolena nabude nakakkaranta hakuri ne dai yayita bayarwa tare da alkawarin bazai karaba . Bayan na ajiye wayan ne. Benaxir ta kimtsa tare dacewa nayi nawa kawas sauran ke yarage. Don Allah ki dage matsalan wani lokacin namu ne. Don munada kishiya sai muke jin tsoron zama kome. Ai bahaka akeba. Kishiya yaruwace. Koda wasa idan kinason zaman lafiya kada kitada hankalinki akan kishiya . Metafiki? Itaba mace bace.? Meye zaki tsaya kina daga hankali. Ko mijinki aure zai kara nasan dole kiji bakin ciki. Anma ne dannewa zakiyi kiyi addua Allah ya rage miki zafin kishi. Kinuna masa bakomai. Hartaxo wallahy kimanki ne zai karu a idonsa. Ko zama kuke yazama na kin zauna da ita zuciya daya .zaman mijinki kikeyi ba itaba akanme zakina bata lokacinki. Ki kimtsa ki gyra. Kwaliyya. Girki . Tsafta. Ladabi da biyayya .hakuri. iya magana wannan sune jinshikin zaman ku. Inkinsa Allah a zuciyanki. Anma in namiji zai kara mace ko da kinada kishiya kiyita damun kanki to fasawa zaiyi? Sannan inkina abu don mijinki yasaki amaryarki. Kintaba ganin yanda namiji yasaki amarya saboda uwargyda? Dasauri nace gani!! Tayi murmushi tace naki dabanne. Don wannan lamin tasan kan makirci . Kidai koyi hakuri kota yaya. Dama shi zaman auren hakuri ake. Duk macen dakika tazama wata shes very proud of herself nd family. Tohfa tayi kuka wa namiji . Kobatayi a fili ba tayi a boye . Namiji haka yagada. Anma dole muyi biyayya. Nifa in kishiya ne yakaro uku. Baidamenba walah suxo muzauna. Na kalli benaxir din dakyau sannan nace. Wallah fada kike . Bakisan zafinsubane. Anandai tamin natsiha sosai. Har naxo nagama kaman nine nayi sake har lami tasamu gangarana.bayan narakata nadawo abba yakiran donjin shawarana acewarsa sulemanu yamasa magana. To acikin haydar da sulemanu wanne ne. Momy na nakalla. Itama kallon nawa take. Sai nace sulemanu. Sai yace Allah yasa albarka ran jummaa idan zaa daura aurensu hauwau zaa hada danaki. Nan jikina yayi sanyi.


==>NIDA KISHIYATA 9 ==>tun lokacin bankarajin duriyar haydar ba. Donhaka sai nayi tunanin ko ya hakura. Ran jumma aka daura aure. Ina zaune benaxir tskirani. To amarya yanxu idan kin koma plx kiyi abinda nace miki. Nayi dariya nace kinmanta gydan sulemani zanje?. Tace a a kam.ke kina matan wani kina maganan wani. Da haidar fa aka daura miki. Wayan hannunane ya subuce. Mikewa nayi zani na kuncewa nayi dakin momy nace momy dawa aka daura auren?. Tace haydar. Nanfa naxube nafara kuka. Momy yazakumin haka. Wlh banson komawa gydansa. Nasiha tayitamin. Ta gwadamun muhimmincin komawa. Sannan takara dacewa kishiya dakika gani yaruwa ce. Kardan kuna zaune kuke samun matsala. Ko ita taki to ki rungumi mijinki .ba zamanta kikeba. Jikina yayi sanyi. Dare nayi a ka kaini nasha mamaki danaga komai na gydan sabo. Kuma ankaramin kayan daki. Komai a kimtse. Nida abulkhair muka yi wanka sannan nabi lafiyan gado. Dasafe yashigo da sallama. Na amsa batare dana kalleshi ba. Guri yanema yazauna sannan yace. Amaryata . Dariya ne ya subucemin sannan nace. Wacce amaryan. Yace gaki. Nace da da kuwa!.anan yakara rokona gafara akan abinda yamin. Nanuna masa ba komai Nan mukacigaba da soyayyanmu. Namanta da wata aba kishiya.anma kullum idan natuna da lami sai nayi dariya sosai.daga baya nakejin labari wai takara aure. Haydar kuwa sabon soyayya ne tashiga tsakaninmu . Gamu ga danmu.
Alhamdulilah.


kuci gaba da ziyaryarmu akoda yaushe domin jin dadinku

COMMENTS

Name

Al'ajabi,13,Android zone,69,Applications,3,Aure,25,Blogger zone,1,computer zone,4,Dadin Kowa sabon salo,27,Facebook zone,12,Free Browsing,2,Hausa Films,1,Hausa novels,1,hotuna,2,Java zone,15,Kannywood,55,kiwon lafiya,35,Mata,12,Musics,24,Network,21,News,146,others,16,siyasa,81,Soyayya,3,Symbian zone,5,Video clips,33,video tutorials,3,Whatsapp,1,
ltr
item
Ameer: [Hausa novels] DOWNLOAD NIDA KISHIYATA COMPLATE
[Hausa novels] DOWNLOAD NIDA KISHIYATA COMPLATE
http://fm.nextwapblog.com/files/6475/nida-kishiyata-icon-001.jpg
Ameer
https://ameeryau.blogspot.com/2017/08/hausa-novels-download-nida-kishiyata.html
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/2017/08/hausa-novels-download-nida-kishiyata.html
true
2994989324915487916
UTF-8
Loaded All Posts Not found any posts VIEW ALL Readmore Reply Cancel reply Delete By Home PAGES POSTS View All RECOMMENDED FOR YOU LABEL ARCHIVE SEARCH ALL POSTS Not found any post match with your request Back Home Sunday Monday Tuesday Wednesday Thursday Friday Saturday Sun Mon Tue Wed Thu Fri Sat January February March April May June July August September October November December Jan Feb Mar Apr May Jun Jul Aug Sep Oct Nov Dec just now 1 minute ago $$1$$ minutes ago 1 hour ago $$1$$ hours ago Yesterday $$1$$ days ago $$1$$ weeks ago more than 5 weeks ago Followers Follow THIS PREMIUM CONTENT IS LOCKED STEP 1: Share to a social network STEP 2: Click the link on your social network Copy All Code Select All Code All codes were copied to your clipboard Can not copy the codes / texts, please press [CTRL]+[C] (or CMD+C with Mac) to copy