Shiga nan domin samun wasu darusan akan abubuwan da suka shafi aure Yawancin mata ba su san dadin aure ba. ’Yan uwa, ko kin san dalilin da y...
Shiga nan domin samun wasu darusan akan abubuwan da suka shafi aureYawancin mata ba su san dadin aure ba. ’Yan uwa, ko kin san dalilin da ya sa ba ki da sha’awa kuma idan mijinki ya kusan ce ki ba kya jin dadi? Sai ki duba ki gani mai yiwuwa wadannan bayanai za su iya ba ku haske a kan matsalar da ke damunku, domin neman mafita. Duk da ya ke an fi ganin cewa, mata sun fi maza yawan sha’awa da son jima’i a yanayin halittarsu a kan maza, ba abin mamaki ba ne a sami akasin haka wani lokacin cewa, akwai mata da yawa wadanda ba su da sha’awa ko kwadayin jima’I, saboda wasu dalilai na lafiya. Hakan na faruwa inda za ka sami mace na gudun kwanciyar aure ko ba ta damu da a yi kwanciyar ko kada a yi ba (duk daya ne a gurinta), saboda ko da an yi ma ba ta jin dadin jima’in sam ko kuma ba ta jin dandanonsa irin yanda ta ke tsammanin a ke ji, kamar yadda sauran mata ‘yan uwanta ke jin dadin rayuwar aure da mazajensu. Tana yin kwanciyar aure ne kawai a matsayin wani aiki na biyan bukatar mijinta ba bukatarta ba, kuma ba don ta na jin dadi ba ko gamsuwa, sai dai kawai don bautar aure ko gudun fushin sabawa al’ada ko addini ko kuma domin kare mijinta daga fadawa tarkon zina. Hakika akwai mata da yawa da su ke cikin wannan yanayin rayuwar aure marar dadi, wadanda sun hakura da hakkinsu na jin dadin aure, inda wasu matan kuma ke kokarin neman mafita daga wannan matsala ta neman hakkinsu daga mazajensu ko neman magani ko ma kokarin fahimtar matsalar da ke hana su jin dadin da nufin neman warwarar matsalarsu. Wannan kalubale ne babba. A nan za mu ari wasu bayanan lafiya, domin bada haske ko bayani a kan wasu daga cikin dalilan da su ka saka wasu mata ba su da sha’awa ko ba sa jin dadin jima’i (salam su ke ji) ko ba sa jin dadi sosai ko kuma ma ba su taba jin dadin ba a rayuwar aurensu. Wasu dalilai na da alaka da macen, wasu kuma namijin ne. Su ne kamar haka: (1) Ciwon Sanyin Mara Ko Matsalolin Mara Da Mahaifa: Kama daga sanyin mara (baginities/toilet infections, UTI da STDs), yoyon fitsari, ‘kululun mahaifa (fibroid) da sauran cututtukan al’aura na daga cikin abubuwan da ka iya hana mace jin dadin jima’i. Misali; sanyin gaba mai zuwa da ’yan kananan kuraje cikin farji na sanya mace ta ji zafi wajen jima’i yayin da da maigida ya ke kusantar ta, wanda sau da yawa masu kurajen ba su ma san su na da kurajen ba cikin al’aurarsu, sai dai su ce su na jin zafi lokacin saduwar. Kurajen su na fashewa, saboda da gugar zakari, sai wurin ya zama rauni. Hakan na sa mata tsoron jima’i da ganinsa a matsayin abin azabtarwa gare su maimakon abin jin dadi. Sau tari ba su san abinda ya haddasa zafin ba, wanda kuma mai yiwuwa ciwon sanyi ne. Ciwon sanyi na iya dakushe sha’awar mace ko namiji. Ciwon sanyi na iya haddasa bushewar gaba, wanda alamunsa shi ne daukewar ni’ima da kaikayin gaba. Idan gaba ya bushe zai yi wahala mace da miji su ji dadin jima’i idan banda zafi. Haka kuma shi ma kululun mahaifa ya kan ci karo da zakari cikin farji, sai mace ta ji wani irin yanayi marar dadi (discomfort) lokacin nishadin aure. Kuma ya na danne mahaifa ya hana haifuwa da kuma sanya yawan zubar jini. Don haka neman magani shi ne mafita. (2) Budadden Gaba: Rashin tsukakken farji yadda zai damki zakari da kyau, domin samar da jin dandanon fata-da-fata a matse ya na hana mace jin dadin jima’i. Budadden gaba kalubale ne da ke sanya raguwar jin dadi tsakanin ma’aurata. Sau da yawa ma’auratan biyu ba za su sami gam



COMMENTS