Powered by Blogger.

'Yan Hausa Film Ba Sa Bata Tarbiya Duk Wanda Kaga Ya Lalace To Lalatacce Ne Tun Daga Gidan Su -inji Sadiq Sani Sadiq

Fitaccen jarumin Kannywood Sadiq Sani Sadiq ya ce kwarewarsa ta iya taka kowacce rawa ce ta sa ya lashe gasar jarumin jarumai sau uku a jere...

Fitaccen jarumin Kannywood Sadiq Sani Sadiq ya ce
kwarewarsa ta iya taka kowacce rawa ce ta sa ya
lashe gasar jarumin jarumai sau uku a jere.
"Idan har Ina cikin Kannywood ni ne zan ci gaba da
lashe gasar jarumin jarumai a ko wacce shekara
saboda ba na wasa da aikina", in ji Sadiq Sani Sadiq,
a tattaunawa ta musamman da BBC Hausa.
Ya musanta zargin da ake yi cewa yana jajircewa a
fim ne domin ya dusashe taurarin jarumai Ali Nuhu da
Adam Zango, yana mai cewa "su iyayen gidana ne
domin kuwa sun taimaka min sosai a wannan harkar.
Ka ga kuwa babu wanda zai ja da iyayen dakinsa."
A cewarsa, "Ni ina yin fim ne a matsayina na Sadiq
Sani Sadiq, kuma ina da kwazo, da jajircewa, da
mayar da hankali sosai a kan aikina, shi ya sa nake
ganin babu wata gasa da za a yi da ba zan lashe ba."
Sadiq Sani Sadiq, wanda ake yi wa lakabi da Dan
marayan zaki, ya kara da cewa yana son dansa ya
gaje shi.
Jarumin ya ce a baya ya yi kiwon karnuka sosai shi ya
sa "da aka sa ni a wani fim a matsayin mafarauci ban
fuskanci wata matsala ba".
"Abin da ya sa nake iya taka ko wacce rawa shi ne, na
yi hulda da mutane daban-daban a rayuwa tun ma
kafin na soma fim. Shi ya sa idan aka sa ni a
matsayin mai sayar da shayi, misali, za ka ga na yi
abin tamkar mai shayin gaske saboda na taba yin
hulda da shi," in ji jarumin.
Sadiq Sani Sadiq ya bayyana zargin da ake yi wa 'yan
fim na neman maza da cewa "karya ce kawai. Ni ban
taba ji ko ganin wanda yake luwadi ba. Kuma na dade
Ina yin fim. Ka ga kuwa tun da haka ne sai kawai in
ce karya da kazafi ake yi mana."
Ya ce ba aikin 'yan fim ne koyar da mutane tarbiya ba
kamar yadda wasu ke hasashe, yana mai cewa, "duk
wanda ya ce 'yan fim sun bata masa tarbiyya da ma
ba shi da ita. Ai tun daga gida ake samun tarbiyya".
©HausaLoaded

COMMENTS

Name

Al'ajabi,13,Android zone,69,Applications,3,Aure,25,Blogger zone,1,computer zone,4,Dadin Kowa sabon salo,27,Facebook zone,12,Free Browsing,2,Hausa Films,1,Hausa novels,1,hotuna,2,Java zone,15,Kannywood,55,kiwon lafiya,35,Mata,12,Musics,24,Network,21,News,146,others,16,siyasa,81,Soyayya,3,Symbian zone,5,Video clips,33,video tutorials,3,Whatsapp,1,
ltr
item
Ameer: 'Yan Hausa Film Ba Sa Bata Tarbiya Duk Wanda Kaga Ya Lalace To Lalatacce Ne Tun Daga Gidan Su -inji Sadiq Sani Sadiq
'Yan Hausa Film Ba Sa Bata Tarbiya Duk Wanda Kaga Ya Lalace To Lalatacce Ne Tun Daga Gidan Su -inji Sadiq Sani Sadiq
https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEhIiISCTJRH4gP9EENsHLHAQI3rdI30uwiYqqonH5_IlKBKtB12YQ5rukPuhLj09WJOvEwLKez6vYfkOwMlrWSkPUJaO26ks6uQWa9FijyPhyphenhyphenfWpLA9tpLvpTHBeFWcXICbjE5xXgPmrcNd/s320/ic-8309.jpg
https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEhIiISCTJRH4gP9EENsHLHAQI3rdI30uwiYqqonH5_IlKBKtB12YQ5rukPuhLj09WJOvEwLKez6vYfkOwMlrWSkPUJaO26ks6uQWa9FijyPhyphenhyphenfWpLA9tpLvpTHBeFWcXICbjE5xXgPmrcNd/s72-c/ic-8309.jpg
Ameer
https://ameeryau.blogspot.com/2019/04/hausa-film-ba-sa-bata-tarbiya-duk-wanda.html
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/2019/04/hausa-film-ba-sa-bata-tarbiya-duk-wanda.html
true
2994989324915487916
UTF-8
Loaded All Posts Not found any posts VIEW ALL Readmore Reply Cancel reply Delete By Home PAGES POSTS View All RECOMMENDED FOR YOU LABEL ARCHIVE SEARCH ALL POSTS Not found any post match with your request Back Home Sunday Monday Tuesday Wednesday Thursday Friday Saturday Sun Mon Tue Wed Thu Fri Sat January February March April May June July August September October November December Jan Feb Mar Apr May Jun Jul Aug Sep Oct Nov Dec just now 1 minute ago $$1$$ minutes ago 1 hour ago $$1$$ hours ago Yesterday $$1$$ days ago $$1$$ weeks ago more than 5 weeks ago Followers Follow THIS PREMIUM CONTENT IS LOCKED STEP 1: Share to a social network STEP 2: Click the link on your social network Copy All Code Select All Code All codes were copied to your clipboard Can not copy the codes / texts, please press [CTRL]+[C] (or CMD+C with Mac) to copy