Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sha alwashi cewa ba zai ba yan Najeriya kunya ba wajen sawa al’umman kasar daga wurare daban-daban da suka...
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sha alwashi cewa ba
zai ba yan Najeriya kunya ba wajen sawa al’umman kasar
daga wurare daban-daban da suka bashi yardarsu. Shugaban
kasar yayi Magana ne a ranar Alhamis, 3 ga watan Janairu a
fadar shugaban kasa da ke Abuja a wajen taron karramawa
na kafofin watsa labaran Najeriya wato Nigerian Media Merit
Award wanda kwamitin amintattu na kungiyar karrama
kafofin watsa labarai ta shirya. Buhari Ya yabawa kokarin
kungiyar sannan ya kara da cewa dama chan ya san
mambobin kungiyar NMMA da dama tun ma kan ya san
cewa zai kasance a wurin. Tsohon Darakta Janar na gidan
talbijin din Najeriya (NTA), Mista Vincent Maduka wanda ya
jagoranci tawagar yace Buhari ya cancanci zama zakaran
shekara “saboda kana mutunta hakkin kafofin watsa labarai
ba tare da kowani shamaki ba”. Ya bayyana cewa a
karkashin Buhari babu kafar watsa labaran da aka rufe,
sannan kuma an bayar da lasisin talbijin din makaranta na
farko ga jami’ar Lagas, karkashin jagorancin shahararren
malamin bangaren karatun jarida, Farfesa Ralph Akinfeleye. VIDEO:- kalli wannan

COMMENTS