Buba Galadima, kakakin kungiyar kamfen din dan takarar Shugaban kasa a jam’iyyar PDP, ya bayyana cewa dan takarar Shugaban kasa na jam’iyyar...
Buba Galadima, kakakin kungiyar kamfen din dan takarar Shugaban kasa a jam’iyyar PDP, ya bayyana cewa dan takarar Shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar zai lallasa Shugaban kasa Buhari da kaso 60 zuwa 40 a arewa. Galadima ya bayyana cewa Atiku zai yi raba daidan kuri’u da Buhari harma a mahaifar Shugaban kasa, wato jihar Katsina. Galadima ya bayyana hakan ne a lokacin da ya bayyana a wani shirin gidan talbijin din Channels, na Politics Today a ranar Lahadi, 3 ga watan Fabrairu. A cewarsa: “Atiku zai kayar da Buhari da kaso 60 zuwa 45. A wajen da za su yi 50-50 jihar Katsina ce. “A kudu maso yamma, zan fada ba shakku cewa mutanen Yarbawa na mutunta shugabanninsu, ba za su yi zabe na bangaranci ba. Yace shugaba Buhari ya ki sanya hannu a dokar zabe saboda yana tsoron shan kashi.

COMMENTS