_________________________________________ Hakika, akwai mutane da dama da ba sa son a rika saka sunan su (tag) cikin hotunan da ba su da ala...
_________________________________________
Hakika, akwai mutane da dama da ba sa son a rika saka sunan su (tag) cikin hotunan da ba su da alaka da su a shafin facebook. Kasancewar wani lokacin za ka ga wasu daga cikin abokan ka na facebook kan saka hoton da wata kila kai a ganin ka ba shi da wata ma'ana ko amfani kuma sai su yi tag din ka cikin hoton, ko da kuwa kai ba ka so. Kuma kaman yadda muka sani, duk hoton da aka yi tag din ka a ciki, zai bayyana a 'profile' din ka ne kai tsaye, wanda hakan ke nufin abokan ka na facebook din za su iya gani, ko da kuwa kai ba ka 'online' ko kuma ka dade ba ka bude facebook din ba. Hakan ne ya sa tuni shafin na facebook ya tanadar da hanya mafi sauki da za ka rika dakatar da duk wani hoton da aka yi tag din ka daga bayyana a 'profile' din ka idan ba ka so. Kasancewar babu hanyar hana yin tag din gaba daya.
Ga yadda ake yi
YiLogin(budo) shafin ka na facebook(a wayar hannu), sai ka nemi wajen da aka saSettings & Privacya kasan shafin. Ko kuma kai tsaye ka bi wannan link' din � Shiga nan
A shafin na 'Settings', za ka ga inda aka saTimeline and Tagging, sai ka latsa shi. Bayan ya bude, za ka ga 'Review posts that friends tag you in before they appear on your Timeline?'. Za ka ga 'on' da kuma 'off', sai ka latsaOn.
Shikenan! Daga yanzu duk lokacin da abokan ka su ka yi tag din ka cikin wani hoto a facebook, to ba zai bayyana a 'Profile' din ka ba. Sai dai za ka ga sanarwa a 'Notifications' din ka cewa wane ya yi tag din ka cikin wani hoto. Idan kana son hoton ya bayyana a 'profile' din ka, sai ka zabi'Add to timeline'. Idan kuma ba ka so sai ka zabi'Hide'.
.
Like & share
COMMENTS